WASANNI
1 minti karatu
Thomas Partey ya koma Villarreal bayan barin Arsenal duk da fara shari'arsa kan zargin fyaɗe
Tsohon ɗan wasan Arsenal ɗan asalin Ghana, Thomas Partey ya koma Villarreal ta Sifaniya bayan barin Arsenal a ƙarshen kakar bara.
Thomas Partey ya koma Villarreal bayan barin Arsenal duk da fara shari'arsa kan zargin fyaɗe
Ɗan wasan mai shekaru 32 zai bar Ingila, inda a aka fara yi masa shari'a kan zargin fyaɗe da wasu mata uka suka masa. / AP
19 awanni baya

Tsohon ɗan wasan Arsenal ɗan asalin Ghana, Thomas Partey ya rattaba hannu kan kwantiragi da Villarreal ta Sifaniya bayan barin Arsenal a ƙarshen kakar bara.

Partey ya koma ne a matsayin kyauta, saboda kwantiraginsa da Arsenal ta ƙare wa’adi ba tare da wani kulob ya saye shi ba. Kwantiragin ta shekara guda ce tare da zaɓin ƙarin watanni 12.

Ɗan wasan mai shekaru 32 zai bar Ingila, inda a aka fara yi masa shari'a kan zargin fyaɗe da wasu mata uka suka masa.

Ranar 4 ga Agusta aka gabatar da Thomas Partey a gaban kotun majistire ta Westminster bisa zargi biyar na aikata fyaɗe da cin zarafin jinsi, amma ya ƙaryata zargin.

An ba da belin Partey bisa sharaɗin zai sanar da ‘yan-sanda kan duk tafiyar da zai yi zuwa ƙasashen waje, awa 24 gabanin tafiyar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us