A cigaban kikikaka tsakanin Barcelona da mai tsaron gidanta Marc-Andre ter Stegen, hukumar La Liga ta ƙi amincewa da rahoto kan jinyarsa.
Barca ta gabatar da rahoton kan lafiyarsa ga La Liga ba tare da sa-hannun ɗan wasan ba, wanda ɗan asalin Jamus ne.
Golan ya ƙi yarda ya saka hannu kan fom ɗin da zai ba da izinin a gabatar da fayil ɗinsa na lafiya ga kwamitin lafiya na hukumar La Liga.
Sai dai matuƙar babu sa-hannun ɗan wasan, hukumar ba za ta ayyana rauninsa a hukumance ba a matsayin doguwar jinya.
Ayyana cewa Stegen zai yi doguwar jinya yana da muhimmanci ga Barca saboda ta haka za ta samu rarar kashi 80 cikin 100 na albashinsa.
Rarar za ta bai wa Barca damar rijistar sabbin ‘yan wasan da ta sayo, wato Joan Garcia da Marcus Rashford.
Iƙirarin Barcelona
Barcelona na iƙirarin cewa akwai togaciyar dokar bayanai wadda ta ba ta damar gabatar da rahoton lafiyar Stegen ba tare da izininsa ba, bisa dalilan da suka shafi ɗaukar aiki.
Sannan Barca ta ce ƙin amincewar Stegen yana cutar da ƙungiyar a harkar kuɗi da gudanarwa. Ga shi ita hukumar La Liga ta doge kan cewa sai da izinin golan.
Likitan kwamitin La Liga, Dr. Jordi Ardevol ya ce, "Izinin ɗan wasan na da muhimmanci kan fayil ɗin lafiyarsa kafin a fita da shi daga ƙungiyar."
Stegen, mai shekaru 34 ya ba da mamaki saboda ƙin amincewa da shirin shugaban Barcelona, Joan Laporta na neman amfani da tsawaitar rashin lafiyar Stegen don shigo da sabbin ‘yan wasa.
Ɗan wasan ya ƙi amincewa da buƙatar, kuma matakin nasa zai iya janyo a ladabtar da Barca da kuma barazanar ƙungiyar ta kai shi kotu.
Rahotanni na cewa Barcelona ta fasa ganawar gaba-da-gaba da Stegen, inda ta fara shirin ɗaukar matakin ladabtarwa kansa.