Real Madrid ta fitar da wata sanarwa da ke neman Hukumar Ƙwallo Ƙafa ta Duniya, FIFA da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Turai UEFA da ka da su bari Barcelona ta buga wasan gasar La Liga da Villarreal a Amurka.
Wasan da aka shirya Barcelona za ta buga da Villarreal a watan Disamba zai iya faruwa a Amurka, bayan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Sifaniya ta riga ta ba da sahhalewarta.
Shugaban hukumar La Liga Javier Tebas ya nuna muradinsa na ganin gasar ƙasar ta yi shuhura a duniya domin samun ƙarin kuɗin shiga.
Sai dai a yanzu Real Madrid ta bayyana adawarta ga wannan shiri.
Sanarwar ta Real Madrid ta bayyana adawarta ga shawarar buga wasan na mako 17 tsakanin Villarreal da Barcelona a wajen Sifaniya.
Lafuzan sanarwar
"Matakin ya zo ne ba tare da neman shawarar ƙungiyoyi da ke buga gasar ba, kuma ya saɓa wa manufofin buga wasa biyu a musayar filayen wasan ƙungiyoyi biyu (wasa ɗaya a gida ɗaya a gidan abokiyar wasa), da saɓa tsarin da bai wa ƙungiyoyin fifiko kan ƙungiyoyin da suke neman fara wannan tsari.” in ji Real Madrid.
Madrid ta kuma tabbatar da cewa ta nemi FIFA ka da ta ba da izinin buga wasan, kuma ta nemi UEFA ta nemi RFEF ta hana buƙatar.
A tarihi dai ba a taɓa buga wani wasan wata babbar gasar Turai a Amurka ba, amma wasu gasanni kamar La Liga da Serie A suna ƙoƙarin sauya hakan a ‘yan shekarun nan.
Hasali ma an buga wasu wasannin Supercopa de Espana da Supercoppa Italiana na ƙasar Italiya a ƙasar Saudiyya a ‘yan shekarun nan.
A yanzu dai, Real Madrid za ta jira ganin ko buƙatarta za ta samu shiga.