WASANNI
1 minti karatu
Man City ta shiga zawarcin golan PSG, Donnarumma yayin da za ta sayar da Ederson
Manchester City ta Ingila ta tuntuɓi PSG ta Faransa game da ɗauko golansu Gianluigi Donnarumma, yayin da Galatasaray ke ƙoƙarin karɓar Ederson.
Man City ta shiga zawarcin golan PSG, Donnarumma yayin da za ta sayar da Ederson
/ Reuters
13 Agusta 2025

Manchester City ta fara ganawa da Paris Saint-Germain don zawarcin golansu Gianluigi Donnarumma, wanda ke son barin Paris.

City na tattaunawa da ɗan wasan ɗan asalin Italiya, duk da daidaitawa da shi ba zai zo da wahala ba, saboda yana da burin sauya kulob a bazarar nan.

Sai dai batun Man City ta iya ɗauko Donnarumma zai dogara ne kan ko ƙungiyar za ta iya sakin golanta Ederson.

Fabrizio Romano ya ce PSG za ta iya neman farashi da zai kai euro miliyan €50, duk da a zahiri ya yi tsada. Amma ya danganta da yadda suka sayar da Ederson.

Baya ga City, ana ƙishin-ƙishin takwararta a Ingila, wato Chelsea na neman Donnarumma duk da ana cewa zancen ya bi ruwa.

Fabrizio Romano ya kuma ce tuni Galatasaray ta Turkiyya ta tuntuɓi Manchester City da tayin ɗaukar Ederson.

A halin yanzu, City za ta fara wasanta na buɗe kakar 2025-26 wannan Asabar ɗin, inda za ta kara da Wolves, kuma a lokacin ne za a ga wanda zai tsare mata raga.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us