GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Hukumar UEFA ta nuna banar saƙo kan Gaza kafin wasan PSG da Tottenham bayan sukar da Salah ya yi
Matakin na zuwa ne bayan da Gidauniyar Yara ta UEFA ta yi shelar cewa za ta taimaka wa yaran da yaƙi ya shafa a yankuna daban-daban na duniya.
Hukumar UEFA ta nuna banar saƙo kan Gaza kafin wasan PSG da Tottenham bayan sukar da Salah ya yi
UEFA ta fitar da sabon saƙo game da Gaza gabannin wasa tsakanin PSG da Tottenham / AA
19 awanni baya

Hukumar ƙwallon ƙafar Turai, UEFA ta nuna wani saƙo a ƙyalle mai alaƙa da yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya. Saƙon na cewa: "A Daina Kashe Yara. A Daina Kashe Fararen-hula", gabannin wasan Super Cup na UEFA tsakanin Paris Saint-Germain da Tottenham.

"Saƙon a bayyane yake ƙarara," cewar UEFA a shafinta na X ranar Laraba. "Wata bana. Wani kira."

Gabannin wasan, wasu yara daga wuraren da yaƙe-yaƙe suka shafa sun ɗaga ƙyallen mai rubutu, ciki har da yara biyu daga Gaza.

Lamarin ya biyo bayan sanarwar Gidauniyar Yara ta UEFA mai cewa za ta taimaka wa yara =n da yaƙe-yaƙe suka shafa a yankuna daban-daban na duniya.

Haka nan lamarin ya zo ne bayan sukar da ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya yi wa hukumar UEFA kan mutuwar Suleiman al-Obeid, da aka fi sani da "Pelen Falasɗinawa", saƙon da bai yi tir ko ambata yadda aka kashe shi a Gaza ba.

A saƙon alhininta a makon da ya gabata, UEFA ta ce al-Obeid ya kasance "ɗan baiwa wanda ya bai wa yara mara adadi kyakkyawan fata har ma a lokutan ƙunci."

Salah ya wallafa saƙo a shafinsa na X da kalaman da ke cewa: "Shin za ku iya gaya mana yadda ya mutu, a ina, da kuma dalilin?"

Sukar tasa, wadda aka kalla sau miliyan 115  tun lokacin da ya wallafa ta, ta janyo wa hukumar ta ƙwallon ƙafar Turai baƙin jini, inda ta ƙauce wa ambaton Isra’ila a kowane mataki.

Ɗan wasan ɗan Masar a halin yanzu ɗaya ne daga cikin ‘yan wasan da suka fi ƙwarewa a tarihin gasar Firimiya, ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza daga farkon kisan ƙare-dangin, tare da kira da a bar kayayyakin jin-ƙai su shiga yankin da aka yi wa ƙawanya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us