A maraicen Lahadi 10 ga Agusta Crystal Palace ta doke Liverpool a bugun ɗurme, inda ta ɗaga kofin Charity Shield na Ingila, wanda ake bugawa tsakanin zakarun gasannin Firimiya da na FA.
Yayin da Crystal Palace ke murnar wannan nasara ta biyu a shekarar nan, a yau kuma ƙungiyar ta shiga baƙin cikin rashin nasara a ɗaukaka ƙarar da ta kai hukumar UEFA game da korar ta daga gasar Europa ta baɗi.
Kotun Sulhu ta Wasanni ta yi hukuncin kan ɗaukaka ƙarar da Palace ta yi game da hana ta buga gasa ta biyu mafi girma a Turai, Europa.
A yanzu Crystal Palace za ta buga gasar Turai ta uku a daraja, ta Conference kamar yadda hukumar ƙwallo ta Turai UEFA ta yanke tun da fari.
Sakamakon hukuncin, Nottingham Forest za ta maye gurbin Palace, saboda ta ƙare kakar bara a mataki na 7 a teburin Firimiya.
Wannan hukunci zai janyo wa Palace asara saboda za ta iya rasa fam miliyan £20 na kuɗin lashe gasa.
Lashe kofin FA
Crystal Palace ce ta lashe kofin FA na Ingila a bara, wanda shi ne babban kofi da suka ci a tarihinsu. Wannan nasarar ce ta ba su garantin shiga gasar Europa kai-tsaye.
Sai dai ana haka sai aka fara taƙaddama kan cewa Crystal Palace na ƙarƙashin mallakar wanɗanda suka mallaki wata ƙungiyar daban, wanda ya sa UEFA ta mayar da Palace zuwa gasar Conference.
Wannan ya harzuƙa Palace inda ta ɗauki matakin shari’a a Kotun Sulhu ta Wasanni, wadda ta yi fatan za ta maido mata da haƙƙinta na buga Europa.
Palace ta sauya mamallakanta kafin wa’adin UEFA na 1 ga Maris ya cika, inda ɗaya cikin mamallakan John Textor sa sayar da hannun jarinsa a ƙungiyar ga Woody Johnson, wanda ya mallaki New York Jets ta Amurka.
A hukuncin nata, Kotun ta kori ƙarar kuma ta ce lallai sai dai Crystal Palace ta buga gasar Conference ta 2025/2026, saboda Textor yana da hannun jari a ƙungiyar Lyon ta Faransa.