Gwamnatin Nijar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da mummunan harin da Isra’ila ta kai a ranar 9 ga Satumba a birnin Doha, babban birnin ƙasar Qatar, wanda harin ya keta mutunci da kuma mutuncin Qatar a matsayinta na ƙasa
A cewar gwamnatin Nijar, “wannan ɗanyen aikin babban kutse ne ga dokokin ƙasa da ƙasa, Kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.”
Bayan nuna tausayawa da kuma nuna goyon baya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Qatar baki ɗaya, Gwamnatin Nijar ta yi kira da babbar murya ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa (musamman MDD) da ta tabbatar an yi hukunci a kan wannan ɗanyen aikin da Isra’ila ta aikata.
A ranar Talata, 9 ga Satumbar 2025, jiragen yaƙin Isra’ila suka kai hari kan manyan jami’an Hamas masu tattaunawar sulhu a birnin Doha na Qatar, inda aƙalla mutum biyar suka rasu.
Baya ga Nijar ƙasashen Afirka da dama da sauran ƙasashen duniya sun yi Allah wadai da wannan hari.