Adadin ma’ikatan agajin da aka yi garkuwa da su a Sudan Ta Kudu ya ruɓanya a wannan shekarar, in ji wasu manyan jami’an agaji biyu na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Ƙungiyoyin agaji sun damu game da rayuwar ma’aikatansu da kuma katse ayyukansu na ceton rayuka a wani yankin da ke fama da ɗaya daga cikin bala’i mai tsanani a duniya.
An sake wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su bayan an biya kuɗaɗen fansa, in ji mutum uku da suke sane da tattaunawar, amma wani ma’aikacin agaji ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane da farkon wanna watan, in ji wasu majiyoyi da suka san da lamarin, ciki har da Edmund Yakani, wani sanannen mai fafatukar kare ‘yancin ‘yan’adam a ƙasar.
MDD ta daɗe da ayyana Sudan Ta Kudu a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fi muni ga ma’aikatan agaji a duniya.
Sai dai kuma, masharhanta sun ce ƙaruwar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa wani sabon salo ne mai tayar da hankali a ƙasar.
“Tashin hankali mafi girma shi ne wannan zai iya zama batun da zai karaɗe ƙasar,” in ji Daniel Akech, wani masani a kan Sudan Ta Kudu da ke aiki da ƙungiyar International Crisis Group.
An fi garkuwa da ma’aikatan jinya a shekarar 2025
Sama da ma’aikatan agajin Sudan Ta Kudu 30 ne aka yi garkuwa da su a wannan shekarar, in ji ma’aikatan agajin biyu.
Wannan ya fi yawan ma’aikatan agajin da aka yi garkuwa da su a shekarar 2024 sau biyu, in ji jami’an biyu.
Ma’aikatan agajin sun yi magana da kamfanin dillalncin labaran The Associated Press da sharaɗin sakaye sunayensu saboda ba a ba su izinin tattauna batun tsaro ba.
Sannan suna tsoron ramuwar gayya kan ma’aikatansu, lamarin da zai iya barazana ga ci gaba da kasancewar ƙungiyoyinsu a ƙasar.
Yaƙi da Sudan Ta Kudu tsakanin sojin ƙasar da ɓangarorin ‘yan adawa ya ƙaru sosai a wannan shekarar.
Lamarin ya janyo wasu daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni tun da a aka gani tun lokacin da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 ta kawo ƙarshen yaƙin basasan da ya kashe kimanin mutum 400,000 kuma aka kafa wamnatin haɗin kai mai rauni.
Wasu masharhanta sun ce arangamar suna da alaƙa da gwagwarmaya a kan wanda zai gaji Shugaba Salva Kiir, yayin da jita-jita ke ƙaruwa game da taɓarɓarewar lafiyarsa.
“Wasu garkuwa da mutane domin dalilan siyasa, kamar tilasta wa mutane shiga (tilastawa fararen hula shiga soji), an shafe shekaru ana yin su, amma garkuwa da mutane domin kuɗin fansa wani sabon abu ne,” in ji Ferenc Marko, wani masani a kan Sudan Ta Kudu.
“Wani yanayi ne mai tayar da hankali da zai iya sa aikin agaji ya zama wani abin da ba zai yiwu ba" a jihohin Central da Western Equatoria, in ji shi.
Wani ma’akacin agaji da aka yi garkuwa da shi ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane
An yi garkuwa da James Unguba, wani ma’aikacin agaji na Sudan Ta Kudu, a watan da ya gabata a ƙaramara hukumar Tambura, a jihar Western Equatoria kuma yam utu ranar 3 ga watan Satumba, in ji mutum uku da suke sane game da mutuwarsa waɗanda suka yi magana kan sharaɗin sakaye sunayensu kamar yadda doka ta tanada.
Mutanen uku sun ce wasu mautena sanye da kayan sojin ƙasar ne suka yi garkuwa da Unguba, wanda ya yi aiki da wata ƙungiyar agaji ta cikin ƙasar.
Ba agane takamamman yanayin da ya janyo mutuwarsa nan take.
Wani mai Magana da yauwn sojin Sudan Ta Kudu ya shaida wa AP cewa ba si da bayani game da mutuwar kuma ya ƙi amsa tambayoyi.
Muhimmin aikin jinƙai
Garkuwa da mutane ya katse ayyukan ceto daga druruwan mutane a wurare masu nisa kusa da kan iyakar Sudan Ta Kudu da Uganda da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya , in ji ƙungiyoyin ba da agaji.
A watan Juli, ƙungiyar ba da agaji ta Doctors Without Borders, wadda aka fi sani da, MSF, ta dakatar da ayyukanta a ƙananan hukumomin Sudan Ta Kudu biyu bayan wasu amsu bindiga sun kama ɗaya daga cikin jam’ianta yayin da yake tafiya cikin wani ayarin motoci da aka saka wa alama a ƙaramar hukumar Yei, a jihar Central Equatoria.
Wannan ya faru ne kwanaki huɗu kawai bayan an yi garkuwa da wani ma’aikacin jinya da ke tafiya cikin motar jinya ta MSF.
“Yayin da muke jajircewa game da ba da kulawa da waɗanda ke buƙata, ba za mu iya ajiye ma’aikatansmu suna aiki a wani wuri mara tsaro ba,” in ji Dakta Ferdinand Atte, shugaban MSF a Sudan Ta Kudu, a wata sanarwa.
Ƙungiyoyi masu makamai ne ke garkuwa da mutane
Jami’an ba da agaji kawo yanzu ba su da tabbacin wane ne ke aikata garkuwa da mutane ba.
Sai dai kuma, Akech wanda ke aiki da ƙungiyar ba da agaji ta International Crisis Group, ya ce yankin yana cike ne da ƙungiyoyi masu makamai da ke neman samun riba cikin sauri yayin da tattalin arziƙi ya ci gaba da ruftawa, kuma ake nuna damuwa game da komawar ƙasar cikin yaƙi.
A watan Maris, an tsare Riek Machar, wanda ke jagorantar ƙungiyar adawa mafi ƙarfi a ƙasar kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin mataimakan shugaban ƙasar a cikin gida bayan wani gungun mayaƙa da ke da ɗan alaƙ da sama galaba a kan wani sansanin soji kusa da kan iyakar ƙasar da Ethiopia.
Tuni dai rundunar sojin ƙasar ta zafafa ƙaddamar da ayyukan soji kan dakarunsa, waɗanda suka haɗu da sauran ɓangarori na ‘yan tawaye, ciki har da National Salvation Front (NAS), wata ƙungiya da ta ƙi sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 kuma take arangama da gwamnati tun wancan lokacin.
“Ba mu sani ba idan NAS ce ta ƙaddamar da waɗannan jerin garkuwa du mutane ko kuma sojojin gwamnati ne,” in ji wani shugabna masu fafatukar kare ‘yancin ɗan Adama Yakani.
“Daga abin da na muka sani, babu wata ƙungiya ɗaya za a ce ita kaɗai ce ke alhaƙin [aikaaikar] ba."
Yayin da MDD da kuma yawancin ƙungiyoyin ba da agaji suka bin manufa na ƙin biyan kudin fansa, iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da suna amfani da wasu mutane na daban ciki har da coci-coci a matsayin masu shiga tsakani domin biyan kuɗin fansa, kamar yadda wasu waɗanda suka san da tattaunawar suka shaida wa AP da sharaɗin sakaye sunayensu.
Ma’aikatan agaji na shan matsin lamba
Daga farko a cikin wannan shekarar, gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta ɗauki matakin rushe hukumar ba da agaji ta Amurka, wadda ta ke ba da kuɗi ga rabin ayyukan agaji a Sudan Ta Kudu.
Masu ba da agaji na Turai sun nuna cewa za su iya rage kuɗin da suke bayarwa su ma.
A halin yanzu dai, hare-hare kan ma’aikatan agaji ya ƙaru sosai a duniya, in ji ƙungiya mai bincike mai zaman kanta Humanitarian Outcomes.
A wani rahoton da ta fitar a cikin watan Agusta, ƙungiyar ta ce shekarar 2024 ta kasance shekarar da ta fi mace-mace a tarihi, inda aka kashe ma’aikatan agaji 383 kuma tashin hankali ya shafi 861, kuma ta yi gargaɗin cewa shekarar 2025 na kan hanyarta ta zama zarce ta.