AFIRKA
1 minti karatu
Shugaban Ghana Mahama ya yi wa fursunoni kusan 1000 afuwa
Sauran sun haɗa da mutum 33 da suke rashin lafiya da mutum 33 da shekaraunsu ya ɗara 70 da mata masu shayarwa biyu da kuma mutum biyu da suka kai ƙara.
Shugaban Ghana Mahama ya yi wa fursunoni kusan 1000 afuwa
Shugaban ƙasar Ghana John Mahama / Others
19 Agusta 2025

Shugaba John Daramani Mahama na ƙasar Ghana ranar Litinin ya yi wa fursunoni 998 afuwa daga cikin fursunoni 1014 da aka gabatar domin afuwar.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ruwaito cewa shugaban ya yi wannan ne bisa shawarar hukumar da ke kula da gidajen yarin ƙasar tare da shawarar Majalisar Magabata ta Ƙasar bisa shashi na 7(1) na kundin tsarin mulkin ƙasar.

Wata sanarwa daga Mista Felix Kwakye Ofosu, mai magana yawun bakin shugaban ƙasar kuma ministan watsa labarai na gwamnatin ƙasar, ta ce a cikin jerin waɗanda lamarin ya shafa akwai mutum 787 da suka aikata laifi a karon farko.

Kazalika sanarwar ta ce akwai mutum 87 da aka yanke wa hukuncin kisa waɗanda za  a mayar da hukuncinsu ɗaurin rai da rai da kuma mutum 51 da za a rage hukuncin ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 20.

Sauran sun haɗa da mutum 33 da suke rashin lafiya da mutum 33 da shekaraunsu ya ɗara 70 da mata masu shayarwa biyu da kuma mutum biyu da suka kai ƙara.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us