Zuwa ranar Talata 19 ga Agustan 2025, ambaliyar ruwa a Nijar ta shafi kimanin mutane fiye da 52,000, kamar yadda Ministan Ababen More Rayuwa na Nijar, Kanar Manjo Salissou Mahaman Salissou ya faɗa.
Kamfanin dillancin labarai na Nijar, ANP ne ya ambato cewa ministan, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Ƙasa don Kiyayewa da Kula da Ambaliya (CNPGI) ya jagoranci taron ranar Talata, a babban ɗakin taro na ofishin Firaminista.
Taron shi ne na biyu da kwamitin ya gudanar, kuma ya mayar da hankali kan rahoton ambaliyar ruwa ta 2024, da halin da ake ciki a yanzu da kuma matakan da ake ɗauka.
Game da ambaliyar shekaran nan ta 2025, zuwa ranar 19 ga Agusta, ambaliya ta shafi unguwanni da ƙauyuka 320 a gundumomi 75, inda ta shafi gidaje 7,229 da jimillar mutane 52,655.
Tun da fari an bayar da tallafin abinci ga magidanta 2,801, kuma mutane 19,612 ne suka amfana da hatsi tan 280.1, wanda ya haɗa da gero, dawa, masara, da shinkafa.
Gyaran tituna
Rahotannin na cewa a halin yanzu ana kan gudanar da bayar da tallafin abinci karo na biyu, wanda ke cim ma gidaje 3,776 da jimillar mutane 27,345.
Game da ambaliyar ruwa ta 2024 kuwa, kwamitin na CNPGI ya jagoranci duka ayyukan kai ɗauki don tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa, da gyara kayayyakin more rayuwa da suka lalace sakamakon ambaliyar.
Ta haka, a ƙarshen Disamban 2024, an cim ma gidaje 205,860 da jimillar mutane 1,505,255 da abin ya shafa a yankuna 8 na ƙasar, wato kusan kashi 99.70% waɗanda aka nufata da taimakon.
Baya ga tallafin abinci, an kuma ɗauki matakan gyara kayayyakin da suka samu lahani, kamar tituna, da makarantu.
Duka-duka, kwamitin na CNPGI ya samu CFA biliyan 12 daga lalitar ƙasa kan ambaliyar 2024, da kuma gudunmawar CFA 236,961,500 daga sauran sassa.