Adadin mutanen da suka mutu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai wani masallaci a garin Malumfashi da ke arewa maso yammacin Nijeriya a ranar Talata, ya kai 50, sannan maharan sun kuma sace fiye da mutum 60, kamar yadda jami’an yankin da mazauna garin suka fada a ranar Laraba.
Tun da fari a ranar Larabar wani mazaunin yankin da kuma wani dan majalisar jiha ya ce adadin wadanda suka mutun ya kai 30 daga 13 da aka fara bayarwa.
‘Yan ta’addan sun kai hari ne kan masallacin a garin Unguwar Mantau a yayin da suke Sallar Asuba, inda masu bibiyar rikice-rikice suka bayyana cewa mutum 13 ne suka fara mutuwa.
“An kashe mutane tara a wurin nan take, sannan wasu da dama sun mutu a yinin ranar. Adadin yanzu ya kai 32,” in ji wani mazaunin yankin mai suna Nura Musa a ranar Laraba.
Wani ɗan siyasa na yankin, Aminu Ibrahim, ya shaida wa Majalisar Dokokin Jihar Katsina a ranar Talata cewa mutane 30 aka kashe.
Wani bayani daga Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gida na Jihar Katsina, Dr Nasir Muazu, ya ce harin na ramuwa ne saboda nasarar da al’ummar Unguwar Mantau suka samu a kwanaki biyu da suka gabata, inda suka yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna suka kashe da dama daga cikinsu.
A halin yanzu, gwamnati ta ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.
Matsalar ‘yan fashi a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na Nijeriya tana zama babban ƙalubale ga tsaro.
Wadannan kungiyoyi sun shahara wajen aikata ta’addanci, kai hare-hare kan kauyuka, sace mutane don neman kudin fansa da kuma kwashe dukiyoyi.
Shugaba Bola Tinubu yana daukar matsaya mai tsauri kan ‘yan fashi da ‘yan ta’adda a Nijeriya domin magance wannan matsala, a cewar jami’an gwamnatinsa.