Masu garkuwa da mutane sun kashe jami’an rundunar NSCDC ranar Juma’a da daddare kuma suka kama wani ma’aikaci ɗan ƙasar China a Okpella da ke ƙaramar hukumar Etsako East a Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma jikkata jami’an rundunar NSDC huɗu da kuma wani farar-hula a lokacin harin, kuma ana yi wa waɗanda suka jikkata a wani asibiti.
Jami’an, waɗanda ke aikin tsaro a kamfanin simintin BUA, na kan hanyarsu ta raka ‘yan China biyar zuwa wurin aikinsu a lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna kusa da ƙofar kamfanin, in ji rahotanni.
Majiyoyi sun ce maharan sun buɗe wuta kan jami’an ne inda suka kashe takwas daga cikinsu nan-take. Sun kama ɗaya daga cikin ‘yan China ɗin, yayin da aka kuɓutar da huɗu.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, wani babban jami’i na rundunar NSCDC na Jihar Edo ya ce ma’aikatan suna aikin rakiya ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin da misalin ƙarfe 10:00 na dare.
“An kashe jami’ai takwas, yayin da biyar suka jikkata. An yi garkuwa da wani ɗan China , yayin da aka kuɓutar da huɗu,” in ji jami’in.
Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi ba-ta-kashi da jami’an NSCDC inda suka yi ta musayar wuta kafin su tsere cikin daji da ɗan ƙasar Chinan.
Jami’in ya ce dakarun tsaro sun bazama neman wanda aka yi garkuwa da shi da kuma tabbatar da cewa an kama ‘yan bindigar.
Kwamandan rundunar NSCDC a Jihar , Gbenga Agun, ya kai ziyara inda lamarin ya auku da kuma jami’an rundunar da suka jikkata asibiti.