Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (DSS) ta rubuta wasiƙa ga kamfanin X Corp, mai shafin sada zumunta na X (wanda ake ce wa Twitter a da), tana mai neman kamfanin ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa inda ya ƙaryata Shugaba Bola Tinubu .
A wata wasiƙar da DSS ta wallafa shafinta na X ranar Asabar, hukumar ta zargi Mista Sowore da yin amfani da saƙonsa na X wajen cin fuskar shugaban ƙasa Tinubu da yi masa rashin mutunci da ba’a.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25 ga watan Agusta, Mista Sowore ya soki ziyarar da shugaban Nijeriya ya kai Brazil da kuma kalaman da shugaban ya yi yayin ziyarar.
“Mai laifi @officialABAT (Bola Tinubu) ya je Brazil inda ya ce babu cin hanci da rashawa a Nijeriya a gwamnatinsa. Ji wani ƙarfin hali na ƙarya ba tare da kunya ba!”— in ji Omoyele Sowore (@YeleSowore) ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2025.
Sai dai a wasiƙar da DSS ta aike wa kamfanin X ta ce waɗannan kalaman sun ɓata wa magoya bayan Shugaba Tinubu rai lamarin da ya sa suka yi zanga-zangar rashin amincewa da kalaman na Sowore a kan titunan ƙasar.
Saboda haka, hukumar ta bai wa shafin X wa’adin sa’o’i 24 domin ya cire kalaman Sowore ko kuma ta ɗauki matakai masu tsauri a kan shafin.
Kalaman Tinubu a Brazil
A lokacin da ya kai ziyara ƙasar Brazil dai, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi a Nijeriya sun kawo ƙarshen cin hanci a ƙasar.
“Sauyen-sauyen da na ƙaddamar tun da na karɓi ragamar mulki a Nijeriya suna tasiri sosai. Zan iya bugun ƙirji kan haka. Daga farko sun ba da wahala. Amma a yau sakamakonsu yana haɓaka,” in ji Shugaba Tinubu.
“Yana daɗa bayyana ga mutane. Mun ƙara yawan kuɗi cikin tattalin arzikinmu. Yanzu babu cin hanci da rashawa. Gwamnan babban bankin [Nijeriya] ya zo nan. Ba sai ka san shi ba kafin ka samu takardun kudin ƙasashen waje da kake buƙata,” in ji shi.
“An kawar da ‘yan bunburutu daga kasuwar musayar kuɗaɗenmu. Ƙofa a buɗe take ga cinikayya shiga cikin sauƙi, fita cikin sauƙi,” a cewarsa.
Martanin Sowore
Shi kuwa mai fafatuka, Omoyele Sowore, wanda hukumar DSS take ƙorafi game da saƙon da ya wallafa ya mayar da martani da saƙon DSS.
“Da safiyar yau, X (wadda ake ce wa Twitter a da) ta tuntuɓe ni a hukumance game da wasiƙar barazana da suka samu daga hukumar DSS mara bin doka game da saƙon da na wallafa kan Tinubu. Ba zan goge saƙon ba,” in ji Sowore a saƙonsa na X.
Abin jira a gani shi ne abin da zai faru bayan wa’adin sa’o’i 24 da hukumar DSS ta bai wa X.
Gwamnatin Nijeriya ta taɓa haramta amfani da shafin X
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka fara samun sa-in-sa tsakanin gwamnatin Nijeriya da kafar sada zumuntar X ba.
Ko tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2022 ma sai da ƙasar ta haramta amfani da shafin na X na watanni bakwai bayan shafin ya goge wani saƙo da shugaban ƙasar Nijeriya na lokacin, marigayi Muhammadu Buhari, ya wallafa a shafinsa na X.
A saƙon nasa da X ya goge Buhari ya ce waɗanda suke neman kafa ƙasar Biafra ba su san irin abin da aka yi ba a lokacin yaƙin basasar Nijeriya kuma gwamnati za ta bi da su ta hanyar da suka fi ganewa.
Bayan goge wannan saƙon ne gwamnatin Nijeriya ta hana amfani da shafin na X a ƙasar, har sai lokacin da shafin ya cika wasu ƙa’idojin da gwamnatin ta gindaya masa.