Dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah, ya soki martanin UEFA dangane da mutuwar Suleiman Al-Obeid, wanda aka fi sani da “Pele na Falasdinawa,” bayan hukumar kwallon kafa ta Turai ta kasa bayyana cewa an kashe shi ne ta hanyar harin Isra’ila yayin da yake jiran abinci na agajin jinkai a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
A cikin wani gajeren rubutu a shafin sada zumunta na X a ranar Asabar, UEFA ta bayyana tsohon dan wasan ƙungiyar ƙasar Falasɗinu a matsayin “wani mai baiwa da ya ƙarfafa gwiwowin yara marasa adadi, har a cikin lokuta mafi muni.”
Sai dai, sakon UEFA bai bayyana yadda ya mutu ba, kuma babu wani kalami na Allah wadai ko kira ga tsagaita wuta.
Salah ya mayar da martani ga sakon da cewa: “Za ku iya fada mana yadda ya mutu, a ina, kuma me ya sa?”
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Falasdinu ta bayyana cewa Al-Obeid, mai shekaru 41, ya mutu ne sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan fararen hula da ke jiran tallafin jin kai a kudancin Gaza.
Salah, wanda ke daya daga cikin manyan taurarin gasar Premier League, mai shekaru 33 wanda asalin ɗan Masar ne, ya taba yin kira a baya don a ba da damar kai tallafin jin kai zuwa Gaza tare da kira ga tsagaita wuta.
Salah ya riga ya kafa tarihi a gasar Premier League, yana matsayi na biyar a jerin masu zura kwallaye mafi yawa a tarihin gasar, inda ya zura kwallaye 186 tare da taimakawa a zura kwallaye 87. Haka kuma, yana ɗaya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasa a duniya a yanzu.
Kisan kiyashi kan ‘yan wasa
Isra’ila ta kashe ‘yan wasa Falasdinawa fiye da 800 tun daga ranar 7 ga Oktoba ta 2023, kamar yadda jami’an Falasdinu suka bayyana.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 1,373 tun daga ranar 27 ga Mayu yayin da suke neman abinci karkashin shirin Gaza Humanitarian Foundation (GHF) da Amurka da Isra’ila suka goyi baya, wanda aka yi Allah wadai da shi a matsayin “tarkon mutuwa.”
Kungiyar Kwallon Kafa ta Falasdinu a cikin wata sanarwa ta ce: “Tsohon dan wasan ƙungiyar ƙasar Suleiman al-Obeid ya yi shahada yayin wani hari da sojojin mamaya suka kai a yayin da yake jiran tallafin jin kai a Zirin Gaza.”
Al-Obeid, mai shekaru 41, wanda aka haifa a Gaza kuma mahaifin yara biyar, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun taurarin tarihin kwallon kafa na Falasdinu. Ya buga wasanni 24 a hukumance ga ƙungiyar ta ƙasa kuma ya zura kwallaye biyu.