WASANNI
1 minti karatu
Fulham na shirin dauko Samuel Chukwueze bayan AC Milan ta saka masa farashi
Rahotanni daga Italiya na cewa AC Milan ta saka wa ɗan wasanta na gaba, Samuel Chukwueze farashi.
Fulham na shirin dauko Samuel Chukwueze bayan AC Milan ta saka masa farashi
/ Reuters
17 awanni baya

AC Milan ta Italiya ta saka wa ɗan wasanta Samuel Chukwueze farashin euro miliyan €25, yayin da Fulham ta Ingila ke tattaunawa don sayan sa.

Farashin da aka sa wa ɗan wasan gaban ɗan asalin Nijeriya za a biya rabi ne a dunƙule, sannan rabin ya zo gwargwadon yadda tattaunawa ta kaya.

Rahotannin na cewa Fulham na kan tattaunawa don neman ɗan wasan mai shekaru 26, kuma suna nuna hanzari don kammala cinikin kan lokaci.

A 2023 ne Samuel Chukwueze ya je AC Milan daga Villarreal, amma yanzu bayan shekaru biyu ya zama kaya a can.

Chukwueze ya ci wa Milan ƙwallaye 8 ne kacal cikin wasanni 69 da ya buga. Shi ne ya ci ƙwallo guda da Milan ta doke Real Madrid a wasan share-fagen da ya gabata.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us