Kalaman da tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya, Taribo West ya yi, inda ya ce ba zai taba bai wa ’ya’yansa shawara su yi wa kasar wasa ba kamar yadda ya yi a baya, suna ci gaba da jawo zazzafar muhawa musamman a shafukan sada zumunta.
A wani bidiyo da kafar yada labarai ta News Central ta wallafa, Taribo West ya soki Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasar (NFF) da kuma gwamnatin Jihar Legas kan cewa sun yi watsi da iyalin marigayin tsohon golan tawagar Super Eagles, Peter Rufai, wanda aka yi jana’izarsa a watan nan.
Taribo dai tsohon dan wasan bayan Super Eagles ne wanda ya taka leda tare da marigayi Peter Rufai, wanda hazikin gola ne, inda suka ciyo wa Nijeriya kofuna a gasanni daban-daban a shekarun 1990 zuwa shekarun 2000.
Da yake jawabi lokacin binne Peter Rufai ranar Juma’ar da ta gabata, Taribo ya bayyana bacin-ransa kan yadda ake mantawa da iyalan taurarin ’yan wasan Nijeriya wadanda suka mutu.
Cikin fushi, Taribo ya ce haka aka yi watsi da iyalan tsofaffin ’yan wasa kamarsu Stephen Keshi da Rashidi Yekini da kuma Thompson Oliha, kuma ya ce wannan ne ya sa gwiwowinsa suka yi sanyi, sannan shi ya sa ba zai taba bai wa ’ya’yansa shawara kan su buga wa Nijeriya wasa ba.
Ya jaddada misali kan iyalan Peter Rufai, wanda ya ce suna kuka suka tuntubi tsofaffin abokan wasan marigayin, suna neman karo-karo don a tara kudin binne tsohon golan Nijeriyar.
Sai dai daga bisani, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF ta fitar da wata sanarwa wadda ta yi kama da martani ga Taribo West. NFF ta ce ta taimaka da kudi wajen binne wasu tsofaffin ’yan wasan Super Eagles da suka rasu, wato Christian Chukwu da kuma Peter Rufai.
Sannan hukumar ta ce tana godiya da gudunmawar da suka bayar, sannan za ta ci gaba da tallafa wa iyalan da suka bari.
Ko da yake yayin da wasu ke zargin gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da tsofaffin ’yan wasan kuma ba ta kyauta musu, akwai wasu masu sharhi da ke ganin idan an bi ta ɓarawo, to ya kamata a bi ta ma bi sawu.
Wato ma’ana su ma ’yan wasan galibinsu sun samu makudan kuɗaɗe, da dimbin damarmakin da ya kamata a ce sun dogara da kawunansu ko bayan da suka yi ritaya.
Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa tsofaffin ’yan wasan da suka zama abin tausayi bayan ritaya, ba su yi tattalin arzikin da suka samu ba ne lokacin da suke wasa a manyan kulob-kulob da ke kasashen Turai.
Za a iya misalai kan shi kansa Taribo West, wanda ya taba taka leda a Inter Milan da kuma AC Milan na Italiya, kamar yadda shi ma marigayi Peter Rufai ya taka leda a ƙungiyoyi daban-daban a Belgium, Netherlands, Portugal, da Sifaniya.
Buga kwallo a manyan kungiyoyin Turai hanya ce ta samun makudan kudi daga kwantiragi, da albashi, da tallace-tallace da ‘taurarin ‘yan wasan kwallo ke samu lokacin ganiyar farin jininsu.
Sannan duk sanda suka lashe kofuna ga kasarsu Nijeriya, ‘yan wasan sukan samu kyautuka daga gwamnatin kasa, da ta jihohi, da masu kudi, inda a kan karrama su da kyautar gidaje da makudan kudi, har ma da lambar yabo.
Irin wannan sallama da ake musu, akwai mamaki a ce bayan shekaru sun dawo suna neman a cigaba da daukar nauyinsu.