Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fenerbahce da ke buga babbar Gasar Turkiyya ta Super League, Fenerbahce ta raba gari da kocinta Jose Mourinho, kamar yadda ƙungiyar ta sanar a ranar Jumma'a.
“Mun rabu da Jose Mourinho, wanda ya kasance kocin tawagar ƙwallon ƙafarmu tun kakar 2024-2025. Muna godiya da ƙoƙarinsa ga tawagarmu kuma muna masa fatan alheri a aikinsa na gaba,” in ji Fenerbahce a cikin wata sanarwa.
Wannan matakin ya biyo bayan fitar da ƙungiyar daga wasannin share fagen Gasar UEFA Champions League a hannun Benfica, kwanaki biyu da suka gabata.
Mourinho, wanda ɗan Portugal ne da ya yi suna da nasarorin da ya samu a Turai, ya samu nasara sau 37, canjaras sau 14, da kuma rashin nasara sau 11 a wasanni 62 da ya jagoranta a dukkan gasanni tare da Fenerbahce.
Taƙaddama
Jose Mourinho wanda tsohon kocin Chelsea, Real Madrid, Inter Milan, Manchester United, Tottenham Hotspur, da Roma ne, ya zo Fenerbahce a watan Yunin 2024.
Ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na biyu a Gasar Lig ta bara, inda suka kasa kawo ƙarshen rashin lashe kofin da suka daɗe suna fama da shi, bayan Galatasaray ta lashe kofin.
Mai shekara 62, Mourinho ya fuskanci ƙalubale da dama a lokacin da yake Istanbul. A watan Afrilu, ya dunguri fuskar kocin Galatasaray, Okan Buruk, bayan sun sha kashi 2-1 a wasan kwata-fainal na Gasar Kofin Turkiyya, inda kuma ya ja hancinsa.
An taɓa cin Mourinho tara saboda kalaman da ya yi bayan wani wasan hamayya mai zafi da Galatasaray, inda ya sake sukar alƙalin wasa na Turkiyya.
Ya zargi alƙali na huɗu a gasar da nuna son-kai. An kuma bayyana kalamansa a matsayin “waɗanda ba su dace da ƙa’idojin wasanni ba.”