WASANNI
2 minti karatu
Boniface na takaicin ciwon gwiwarsa bayan da AC Milan ta fasa karbar sa aro
Ɗan wasan Leverkusen ɗan asalin Nijeriya, Victor Boniface yana takaicin ciwon gwiwar da yake fama da shi, bayan da AC Milan ta fasa karɓar sa aro.
Boniface na takaicin ciwon gwiwarsa bayan da AC Milan ta fasa karbar sa aro
/ AFP
17 awanni baya

Victor Boniface, ɗan wasan Leverkusen ta Jamus ya amayar da zuciyarsa kan batun jinyar gwiwa da yake fama da shi tsawon lokaci.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin Nijeriya ne ya samu koma baya, bayan da AC Milan ta Italiya ta mayar da shi gida bayan ya je can da shirin zaman aro.

Boniface ya yi gwaje-gwajen lafiya kafin Milan ta amince da karɓar sa, amma sai ta tura shi gida, wanda ke nufin bai ci gwajin lafiyar da aka masa ba.

AC Milan ta yi niyyar ɗaukar sa aro kan euro miliyan 5, da zaɓin sayan sa kan euro miliyan €24. Amma yanzu cinikin ya ɓare.

Da yake takaicin halin da yake ciki, Boniface mai shekaru 24 ya ce 'Na kusa na ce na daina ƙwallo kwata-kwata’, sakamakon jinyar.

Ƙarewar tagomashi

A 2023 Boniface ya zo Leverkusen ne daga Union Saint-Gilloise ta Belgium, kuma ya yi tasiri a ƙungiyar inda ta lashe kofin Bundesliga na shekarar a karon farko.

Ya ci ƙwallaye 21 a wasanni 34, inda suka ɗaga kofin DFB-Pokal, sannan suka zo na biyu a gasar Europa.

Sai dai Boniface ya ji rauni a tantanin ƙasan gwiwarsa a kakar 2018-19, da kuma 2020-21, kuma raunin ya ci gaba da damun sa.

A kakar bara ya gaza buga wasanni 14 saboda matsalar kuzari. Ga shi yanzu ya gaza cin gwajin lafiya wadda ta hana shi tafiya Italiya.

Boniface ya ce, "Tafiyata ba ta yiwu ba saboda jinyata ta baya. Na samu raunuka biyu a gwiwata ta dama, kuma matsalar ta ci gaba tsawon lokaci. Akwai lokacin da na taɓa tunanin haƙura da ƙwallo.”

Daraktan wasanni na Leverkusen, Simon Rofles ya faɗa wa jaridar BILD cewa, ”Idan [Boniface] ya dawo [Leverkusen], cinikin da Milan ya rushe kenan. Ba abin ɓoyewa ba ne."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us