Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wata tattaunawa mai zafi ta waya da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda ya bayyana "babban takaicinsa" kan yadda aka shammace shi game da harin da Isra'ila ta kai kan wakilan Hamas a Qatar, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito.
A wani rahoto na musamman da aka wallafa a ranar Laraba, Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa Trump ya shaida wa Netanyahu cewa matakin da ya ɗauka kan kai hari kan shugabannin siyasa na kungiyar Falasdinawa a Doha, babban birnin Qatar, babu hikima a ciki. Ya kuma bayyana cewa "ya fusata sosai da jin labarin harin daga sojojin Amurka—maimakon daga Isra'ila—kuma hakan ya faru a yankin wata abokiyar ƙawancen Amurka wanda ke shiga tsakani don kawo karshen yakin Gaza."
Netanyahu ya shaida wa Trump cewa ya samu wata ‘yar ƙaramar dama ce ta kai wa Qatar hari inda ya yi amfani da damar.
Bayan wannan tattaunawar, an sake kiran waya na biyu a tsakaninsu inda aka yi wayar a cikin lumana, inda Trump ya tambayi Netanyahu ko harin ya yi nasara. Netanyahu bai iya bayar da tabbacin nasarar ba.
Daga baya, Hamas ta tabbatar cewa shugabanninta sun tsira daga harin, yayin da mambobi biyar na kungiyar da wani jami'in tsaro na Qatar suka rasa rayukansu.
Trump ya fusata da Netanyahu
Ko da yake Trump ya shahara da kasancewa babban mai goyon bayan Isra'ila, yana kara nuna takaici da Netanyahu, wanda ke ci gaba da sanya shi cikin matsala ta hanyar daukar matakai masu tsauri ba tare da tuntubar Amurka ba, wanda hakan ke saba wa manufofin Trump na Gabas ta Tsakiya, kamar yadda WSJ ta ruwaito.
Rahotanni makamantan haka sun nuna cewa jami'an Fadar White House sun fara gajiya da yadda Netanyahu ke daukar matakai kamar "mai hauka" bayan harin da aka kai a Syria a watan Yuli.
Qatar ta yi Allah wadai da harin, tana mai kiransa da "aikin rashin kunya" da kuma take dokokin kasa da kasa, tana gargadin cewa ba za ta lamunci halayen Isra'ila na "rashin hankali" ba.
Kasar Gulf din, tare da Amurka da Masar, tana taka muhimmiyar rawa wajen kokarin shiga tsakani don kawo karshen kisan kiyashin Isra'ila a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 64,600 tun watan Oktoban 2023.
Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya bayyana a ranar Laraba cewa ana shirya martani na hadin gwiwa daga yankin don mayar da martani ga harin Isra'ila a Doha, yana mai jaddada cewa ana ci gaba da tattaunawa da abokan hulda na Larabawa da Musulmi.
"Akwai martani da zai zo daga yankin. A halin yanzu ana tattaunawa da kuma tuntuɓa game da martanin tare da sauran abokan hulɗa daga yankin," in ji Al Thani ga CNN.