GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
'Tantirai maƙiya Musulunci' ke kula da rabon agaji a Gaza a halin yanzu: UNRWA
Shugaban UNRWA ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya koka kan yadda wata ƙungiya da Isra'ila ta kafa sannan take samun goyon bayan Amurka ta karɓi ragamar jagorancin rabon tallafi a Gaza.
'Tantirai maƙiya Musulunci' ke kula da rabon agaji a Gaza a halin yanzu: UNRWA
Philippe Lazzarini ya jaddada cewa magance yunwa a Gaza na buƙatar samun damar kai tallafi ba tare da tsangwama ba / Reuters
11 Satumba 2025

Shugaban Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinu (UNRWA) ya bayyana cewa tsarin rarraba tallafin da ake yi a Gaza a halin yanzu yana ƙarƙashin kulawar wasu sojojin haya, daga ciki har da wasu da ya kira “tantirai maƙiya Musulunci.

Philippe Lazzarini ya jaddada cewa magance yunwa a Gaza “na buƙatar samun damar kai tallafi ba tare da tsangwama ba, a cikin yanayi mai aminci da kuma a duk inda ake buƙata.”

“Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da UNRWA da abokan hulɗa, suna da kayan aiki da ƙwarewa. Ku bar mu mu yi aikinmu,” in ji shi.

Tun daga ranar 27 ga Mayu, Isra'ila ta kafa wata hanyar rarraba tallafi ta daban ta hanyar abin da ake kira Gaza Humanitarian Foundation, wanda Amurka ke goyon baya amma Majalisar Dinkin Duniya da Falasɗinawa suka ƙi amincewa da ita, suna kiranta da “tarkon mutuwa.”

Isra'ila ta kuma rufe dukkan hanyoyin shiga Gaza tun daga ranar 2 ga Maris, inda ta rinƙa hana abinci, magunguna da kayan agaji shiga, wanda hakan ya jefa yankin cikin yunwa duk da cewa manyan motoci cike da kayan agaji suna taruwa a kan iyakokinta.

Sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai hare-hare masu tsanani a Gaza, inda suka kashe aƙalla Falasɗinawa 64,700 tun daga watan Oktoba 2023.

Wannan farmakin soja ya lalata yankin, wanda yanzu haka ke fuskantar yunwa wadda ayyukan Isra’ila ta haifar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us