Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kaɗa kuri'a a ranar Juma'a kan “Sanarwar New York,” matakin da aka tsara don farfado da shirin samar da zaman lafiya ta hanyar kafa kasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasdin - inda karara aka yi watsi da Hamas a cikin sa.
Sanarwar da a hukumance aka ba wa taken ''Sanarwar Bayan Taron New York, Kan Batun Warware Tambaya Game da Falasdin Cikin Zaman Lafiya da Aiwatar da Mafitar Kasashe Biyu”, kudirin ya yi kira ga hadin kai don kawo karshen yakin Gaza, sannan a samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu ta hanyar kafa kasashe biyu.
Sanarwar ta tabbatar da keɓe Hamas a matsayin ɗaya daga cikin jigon ka’idojin ayyukansu. Ta ce "Dole Hamas ta saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su" tare da yin Allah wadai da "harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba."
Haka kuma, ta bukaci kungiyar Hamas da ta kawo karshen mulkinta a Gaza, tare da mika makamanta ga gwamnatin Falasdinu, tare da goyon bayan kasashen duniya, a wani bangare na hanyar kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Sanarwar ta kuma tanadi yiwuwar jibge tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa ta wucin gadi karkashin umarnin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don tallafawa al'ummar Falasdin da saukaka ayyukan tsaro ga Hukumar Falasdin.
"Mun goyi bayan tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa na wucin gadi bisa gayyatar da Hukumar Falasdinu ta yi, kuma a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya da kuma daidai da ka'idojin Majalisar, bisa la'akari da karfin Majalisar, wanda kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya ya umarta, tare da goyon bayan yanki da na kasa da kasa. Mun yi maraba da shirye-shiryen da wasu kasashe mambobin kungiyar suka bayyana don ba da gudunmawar dakaru, "in ji kudurin.
Rubutacciyar sanarwar da Faransa da Saudiyya suka gabatar, tuni kungiyar kasashen Larabawa ta amince da shi, kuma kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 17, ciki har da kasashen Larabawa da dama ne suka sanya hannu a kai a watan Yuli.
Rashin tabbas na ci gaba da wanzuwa
Jefa kuri'ar ya zo ne gabanin wani babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York a ranar 22 ga watan Satumba, wanda Faransa da Saudiyya za su jagoranta, inda shugabannin Faransa, da Birtaniya, da Canada, da Portugal, da wasu kasashe da dama suka yi alkawarin amincewa da kasar Falasdinu a hukumance.
Ana sa ran wasu shugabannin da dama za su yi irin wannan sanarwar, matakin da ake ganin wata hanya ce ta kara matsin lamba ga Isra'ila na ta kawo karshen yakin da ta ke yi a Gaza, wanda aka kwashe kusan shekaru biyu ana gwabza fada.
A cewar sanarwar New York, "Gaza wani yanki ne mai mahimmanci na kasar Falasdinu kuma dole ne a hade shi da Yammacin Kogin Jordan. Dole ne a tabbatar da ba a samu mamaya, kawanya, rage girman yankuna, ko gudun hijira ala tilas ba."
Sai dai kuma, batun ya kasance mai tsauri da rashin tabbas. Kusan kashi uku cikin hudu na kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 sun riga sun amince da kasar Falasdinu da aka ayyana a shekarar 1988.
Amma, bayan shafe shekaru biyu ana gwabza kazamin yaki a Gaza, fadada matsugunan Isra'ila a yammacin gabar kogin Jordan, da kuma alkawuran da jami'an Isra'ila suka yi na mamayar yankin, ana fargabar cewa ba za a yi nasarar cim ma burin samar da kasashe biyu ba.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashi a ranar Alhamis cewa: "Za mu cika alkawarinmu cewa ba za a taba samun kasar Falasdinu ba."
Shi kuwa Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, mai yiyuwa ne a hana shi halartar taron na New York bayan hukumomin Amurka sun nuna za su hana shi biza ba.