WASANNI
2 MINTI KARATU
Lisandro Martinez: Dan kwallon Man Utd ba zai sake buga wasa a kakar bana ba
Dan kwallon mai shekara 25 ya ji rauni a wasan da Manchester United da Sevilla suka tashi 2-2 ranar Alhamis a gasar Europa League.
Lisandro Martinez: Dan kwallon Man Utd ba zai sake buga wasa a kakar bana ba
Lisandro Martinez ya karye ne a fafatawar da Man Utd da Sevilla suka tashi 2-2 a gasar Europa ranar Alhamis / Others
14 Afrilu 2023

Dan wasan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake buga wasa ba a kakar bana bayan ya karye a kafarsa.

Kulob din ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Juma'a.

Dan kwallon, mai shekara 25, ya ji rauni ne a wasan da Manchester United da Sevilla suka tashi 2-2 ranar Alhamis a gasar Europa League.

"Amma ana sa rai dan wasan dan kasar Argentina zai warke sarai a kan lokaci domin ya soma wasa a kaka mai zuwa," in ji kulob din.

Shi ma Raphael Varane ya ji rauni lokacin wasan kuma ana sa rai zai kwashe makonni yana jinya.

"Dukkanmu a Manchester United muna yi wa Lisandro da Rapha fatan samun sauki cikin gaggawa," a cewar sakon da kulob din ya wallafa.

United ya sayi Martinez Ajax a watan Yulin da ya gabata a kan kusan £57m kuma bug wa kulob din wasan Firimiya 27 a kakar bana.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda, TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us