WASANNI
2 minti karatu
Rodri da Ederson sun warke, za su buga wa Manchester City wasansu da Tottenham - in ji Pep Guardiola
Kocin Man CIty, Guardiola ya ce har yau ‘Rodri shi ne gwarzon ƙwallo na duniya”, yana mai cewa ɗan wasan zai buga musu wasan nasu na gaba da Spurs ran Asabar mai zuwa.
Rodri da Ederson sun warke, za su buga wa Manchester City wasansu da Tottenham - in ji Pep Guardiola
/ Reuters
22 Agusta 2025

Yayin da Manchester City ta buga wasanta na farko a kakar gasar Firimiya ta bana tare da Wolves, golanta Ederson da tauraron ɗan wasanta Rodri ba su samu halartan wasan ba.

Ederson ɗan asalin Brazil ya yi fama da ciwon ciki, inda madadinsa, James Trafford ya yi ƙoƙari sosai kuma ba a ci shi ba a wasan da suka doke Wolves da ci 4-0.

A baya an yi tararrabi kan makomar Ederson a tawagar City, musamman bayan zuwan Trafford, wanda ɗan makarantar koyar da ƙwallo ta Man City ne, wanda ya dawo ƙungiyar bayan kwashe shekaru biyu a Burnley.

Mai shekaru 32, Ederson ya samu tayi daga manyan ƙungiyoyi kamar Galatasaray, amma a yanzu zai yi fatan samun gurbi a tawagar koci Pep Guardiola don ganin bai bar shi yana ɗumama benci ba.

Wasan City na gaba tare da Tottenham yana da ban tsoro saboda City ta sha kashi a hannunsu sau tara a duka gasanni, kuma idan ban da Liverpool babu wanda ya taɓa doke su da yawa haka.

Rodri gwarzon duniya

Kocin Man CIty, Guardiola ya ce har yau ‘Rodri shi ne gwarzon ƙwallo na duniya”, yana mai cewa ɗan wasan zai buga musu wasan nasu na gaba da Spurs ran Asabar mai zuwa.

Rodri wanda shi ke riƙe da kambin gwarzon ɗan ƙwallo na duniya na Ballon d’Or, bai samu buga wasan City na farko ba.

Ɗan asalin Sifaniya, Rodri yana farfaɗowa ne daga jinyar tiyatar ACL da aka masa tun kakar bara, inda wasanni uku kacal ya buga a kakar ta 2024-25.

Ya dawo tawagar a gasar Kofin Duniya ta Kulob-kulob amma sai ya sake tafiya jinya.

Guardiola ya faɗa wa manema labarai cewa, “Rodri da Phil ba su buga mana wasan baya ba, amma saboda dalili ɗaya ne - rashin atisaye, ba su je Palermo ba yayin da sauran tawagar ke wasannin share fagen kakar bana.

“Ba za su iya buga mintuna 90 a karawarmu da Wolves ba, amma yanzu sun shirya kuma tabbas za su buga gobe.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us