AFIRKA
2 minti karatu
Attajirai za su ƙara yawa a Afirka cikin shekaru goma masu zuwa - Rahoto
Afirka Ta Kudu ce ke da kashi 34 cikin 100 na attajiran Afirka yayin da yawan attajiran Nijeriya ya ragu sosai, in ji Rahoton Arziƙin Afirka.
Attajirai za su ƙara yawa a Afirka cikin shekaru goma masu zuwa - Rahoto
Ana sa ran adadin 'yan Afirka masu aƙalla dala miliyan ɗaya zai ƙaru da kashi 65 cikin 100 cikin shekaru 10 masu zuwa. / Others
11 awanni baya

Adadin yawan ‘yan Afirka masu miliyoyin daloli zai ƙaru da kashi 65 cikin 100 cikin shekaru goma masu zuwa, in ji Rahoton Arziƙi a Afirka na shekarar 2025.

A halin yanzu nahiyar na da attajirai na biloniyoyin daloli har mutum 25 da kuma mutum 348 masu aƙalla dala miliyan 100 da kuma mutum 122,500 masu aƙalla dala miliyan ɗaya, in ji rahoton shekara-shekara da kamfanin Henley & Partners mai sa ido a kan arziƙi ya wallafa.

An yi ƙiyasin cewa tattalin arziƙin Afirka ta Kudu da Hamadar Sahara zai ƙaru da kimanin kashi 3.7 cikin 100 a shekarar 2025 — inda za ta zarce Turai (mai kashi 0.7 cikin 100) da Amurka (mai cikin 1.4 cikin 100) — inda ake hasashen cewa girman tattalin arziƙi zai kai kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2026.

A halin yanzu Afirka ta Kudu ce ke da kashi 34 cikin 100 na masu dala miliyan ɗaya a Afirka — kusan daidai yawan attajiran ƙasashe biyar da ke biye da ita da yawan masu arziƙi a nahiyar — da masu aƙalla dala miliyan 41,100.

Ƙasar tana kan gaba a cikin ƙasashen Afirka biyar da suka fi ƙarfin tattalin arziƙin da suka haɗa da Masar (mazauna 14,800 masu aƙalla dala miliyan ɗaya) da Morocco (mai mazauna 7,500 masu aƙalla daka miliyan ɗaya) da Nijeriya (mazauna 7,200 masu aƙalla dala miliyan ɗaya), da kuma Kenya (mai mazauna 6,800 masu aƙalla dala miliyan ɗaya ), wanda gaba ɗaya suka kai kashi 63 cikin 100 na attajiran nahiyar masu aƙalla dala miliyan ɗaya da kuma kashi 88 cikin 100 na masu aƙalla dala biliyan ɗaya.

Adadin ‘yan Nijeriya masu aƙalla dala miliyan ɗaya ya ragu da kashi 47 cikin 100, inda adadin ya kuma ragu a Angola da Aljeriya.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us