Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
RAYUWA
3 minti karatu
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a DauraBikin na 2025 wanda ya yi daidai da cika shekara 10 da samar da ranar, ya ƙayatar matuƙa, inda aka yi shi a garuruwan duniya, ciki har da babban taro a garin Daura “Tushen Hausa”, wanda ke Jihar Katsinan Nijeriya.
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura / Others
10 awanni baya

Kamar yadda aka saba tun daga 2015, ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake gudanar da bikin Ranar Hausa a faɗin duniya.

Bikin na shekarar nan ta 2025, ya yi daidai da cika shekara 10 da samar da ranar. Bukukuwan da aka yi a garuruwan daban-daban na duniya sun ƙayatar matuƙa.

An yi babban taro a garin Daura “Tushen Hausa”, wanda ke Jihar Katsinan Nijeriya, inda Mai Martabaa Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk ya karɓi baƙuncin shagulgulan.

Bikin ya kuma samu halartar gwamman Jihar Katsina, wanda Usman Abba Jaye ya wakilta, da kuma wakilin Firaministan Nijar kuma gwamnan Damagaram, Masallaci Umar da kuma Sultan na Damagaram, Aboubacar Oumarou Sanda.

Akwai kuma wakilan Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya har ma da wakilan Majalisar Dinkin Duniya.

An gabatar da wasannin al’adun Hausawa da dama a yayin bikin, kamar su kokawa da wasan maƙera na wuta da hawan daba.

Hawan dabar da aka yi ya nuna tawagogin ƙasashen Hausa Bakwai da na Ƙanne Bakwai (wanda yanzu ake kira Banza Bakwai), waɗanda suke da tushe a tarihin Hausawa na Daura da Bayajidda.

Daga manyan mawaƙan Hausa da suka gwangwaje bikin Ranar Hausa na 2025 akwai tauraruwar mawaƙiya Fati Nijar da ta yi waƙa a bikin na Daura.

Jawabin taro

Tun gabannin ranar bikin, manyan mutane da dama a yankunan ƙasar Hausa sun goyi bayan hidimar ta bana, ciki har da Firaministan Nijar Ali Lamine Zain, da Ministan Al’adu da na Matasa na Nijar, Mr. Sidi Mohamed Almahmoud, da Ministar Al’adun Nijeriya, Hannatu Musawa da Gwamnan Katsina, Umaru Radda, da Sarkin Daura Umar Faruk.

Jagoran bikin na Daura, wanda kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiri ranar, Abdulbaƙi Aliyu Jari, wanda kuma ma’akacin TRT Afrika ne, ya kai ziyarar ban-girma ga waɗannan jagororin al’umma, inda ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa bikin na bana zai fi armashi kasancewarsa karo na 10.

Abdulbaki Jari ya kuma yi kira ga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS da ta mayar da harshen Hausa ya zama wanda ake harkokin kasuwanci da shi, da ma mu’amalar zamantakewa a hukumance a yankin.

Jari ya ce, amfani da harshen Hausa wajen kasuwanci da cinikayya zai ƙarfafa zamantakewar tattain arziƙi da inganta sadarwa a tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka.

Ranar Hausa ta bana na da nufin ƙarfafa harshen Hausa da al’adu da girmama ɗimbin  gudunmawar da al’ummomin da ke magana da Hausa aƙalla ƙasashe 25 ke bai wa tattalin arziƙi.

Tasirin harshen Hausa

Hausa shi ne harshen da ya fi yawan jama’a masu amfani da shi a Yammacin Afirka, wanda sama da mutum miliyan 100 suke magana da shi a faɗin duniya. Harshen Hausa ya samu ne daga ajin harsunan Afirka-Asiya.

Harshen Hausa ya fi yaɗuwa ne a yankunan Nijeriya, da Nijar, da Ghana, da Chadi, da Benin, da Kamaru, da Togo, da Gabon, da Sudan, da Saudiyya, da Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wannan ya faru ne sakamakon ɗaruruwan shekaru na tafiye-tafiye cikin yankunan kudancin Sahara, wanda mahajjata da ‘yan ci-rani suka yi don neman arziƙi da wadata.

A yau, harshen Hausa, ya zama harshen gamagari, inda miliyoyin mutane suke mu’amala da harshen a gidajensu, da maƙwabtansu, da sauran mutanen duniya.

Hausa ya zama wata magama tsakanin masu amfani da harsuna daban-daban a faɗin Afirka. Amurka da sauran ƙasashen Turai ma ba a bar su a baya ba wajen amfani da Hausa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us