NIJERIYA
2 minti karatu
Shugaba Tinubu ya dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanya daga Nijeriya
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X Shugaba Tinubu ya ce: “Mu muke samar da kashi 40 cikin 100 [na ƙwallon kaɗanya ] a duniya, duk da haka muna samun ƙasa da kashi 1 cikin 100 na darajarsa a kasuwa duniya da ta kai dala biliyan 6.5.”
Shugaba Tinubu ya dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanya daga Nijeriya
Ƙasashen Afirka da dama suna fitar da ɗanyen kayayyaki da ba a sarrafa ba inda suke samun kaɗan daga cikin darajar kayayyakin bayan an sarrfa su / AP
8 awanni baya

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya haramta fitar da ƙwallon kaɗanya daga ƙasar wanda shugaban ya bayyana a matsayin “koren arzikin,” ƙasar.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X shugaban ya ce: “Mu muke samar da kashi 40 cikin 100 [na ƙwallon kaɗanya ] a duniya, duk da haka muna samun ƙasa da kashi 1 cikin 100 na darajarta a kasuwa duniya da ta kai dala biliyan 6.5.”

“Daga yanzu rashin daidaiton ya zo ƙarshe. Na amince da dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanya na tsawon wata shida bisa shawarar kwamitin da ke bai wa shugaban ƙasa shawara game da harkar abinci, domin samar da man ga masu sarrafa shi a cikin gida da samar da ayyukan yi da kuma kare wani fannin da kashi 95 na masu aiki a ciki mata ne,” in ji shugaban.

“Wanann nasara ce ga manomanmu da matanmu da ma Nijeriya. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai yi aiki da masu ruwa da tsaki a lamarin domin faɗaɗa ikon sarrafa [man] cikin sauri da kuma tabbatar da cewa wannan sauyin zai kawo wadata,” a cewar Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa yadda hanyar ciniki ke buɗewa a Brazil da ma wasu ƙasashe, ƙasar za ta fara samun ƙarin kuɗin shiga daga kayayyakin da take samarwa.

 Za mu samar da ababe masu daraja a gida, mu yi gogayya a ƙetare kana mu samar da wadata a ƙarƙashin manufa ta Sabon Fata.

Ƙasashen Afirka da dama suna fama da matsalar fitar da ɗanyen kayayyaki da ba a sarrafa ba inda suke samun ɗan kaɗan daga cikin abin da za a iya samu daga kayayyakin bayan an sarrafa su.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us