AFIRKA
2 MINTI KARATU
An kashe sojojin Nijar 12 a wani harin kwanton-bauna
An kai harin ne kan sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa da ke yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yayin wani samame da suka kai ranar Lahadi da yamma a garin Anzourou.
An kashe sojojin Nijar 12 a wani harin kwanton-bauna
Martanin da dakarun sojin suka mayar ya jawo asarar rayuka sosai a gwabzawar. Hoto: Reuters Archive / Reuters Archive
22 Agusta 2023

Ana zargin masu ikirarin jihadin sun kashe sojojin Nijar 12 a kudu maso yammacin yankin Tillaberi, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ruwaito.

An kai harin ne kan sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa da ke yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yayin wani samame da suka kai ranar Lahadi da yamma a garin Anzourou, a cewar gidan talabijin na Tele Sahel.

"Martanin da dakarun sojin suka mayar ya jawo asarar rayuka sosai a gwabzawar," in ji gidan talabijin din.

Hakan na faruwa ne kasa da mako guda da kai harin kwanton bauna yankin Tillaberi, inda aka kashe sojojijn Nijar 17, sakamakon wani hari da shi ma ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai shi kan iyakar Mali.

Ga wasu labaran masu alaka

MAJIYA:AFP
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us