AFIRKA
2 MINTI KARATU
'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban Guinea daga gidan yari
'Yan bindiga sun afka babban gidan yarin Conakry inda suka saki tsohon shugaban kasar Moussa Camara.
'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban Guinea daga gidan yari
Moussa Camara ya koma gida daga gudun hijira a 2021. Hoto/AP / Others
4 Nuwamba 2023

Wasu ‘yan bindiga sun dauke tsohon shugaban Guinea Moussa Dadis Camara daga gidan yari, kamar yadda ministan shari'a na kasar Charles Alphonse Wright ya bayyana.

Sanarwar ministan na zuwa ne bayan an shafe sa'o'i ana jin karar harbe-harben bindiga a birnin Conakry.

Lauyan tsohon shugaban kasar Jocamey Haba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yana zaton an dauke wanda yake karewa ba da son ransa ba daga gidan yarin.

Dama tun safe an ta jin karar harbin bindiga mai karfi a tsakiyar Conakry babban birnin Guinea, kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka yi kawanya a sashen da ake harbe-harben.

Kanal Mamady Doumbouya shi ne ke jagorantar Guinea wanda ya karbi mulkin kasar bayan an shafe shekara 11 ana mulkin dimokuradiyya.

MAJIYA:AFP
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us