TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Majalisar Dokokin Turkiyya za ta daina sayen kayayyakin kamfanonin da ke goyon bayan zaluncin Isra'ila
Wannan mataki na zuwa ne don mayar da martani ga hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke yi kan yankin Gaza na Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya, inda aka kashe a kalla Falasdimawa 10,328 tun daga 7 ga Oktoba zuwa yanzu.
Majalisar Dokokin Turkiyya za ta daina sayen kayayyakin kamfanonin da ke goyon bayan zaluncin Isra'ila
"Ba za mu sayi wani abu ba kuma za mu jefar da wanda muka saya," in ji shugaban majalisar dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus. / Hoto: AA / Others
7 Nuwamba 2023

Majalisar dokokin Turkiyya za ta daina amfani da kayayyakin da kamfanonin da ke goyon bayan hare-haren da Isra'ila ke yi, suka samar," in ji shugaban majalisar.

A yayin da yake jawabi a wajen wani taro a yankin Ordu na arewacin Turkiyya, Numan Kurtulmus ya bayyana cewa "A Babbar Majalisar Dokokin Turkiyya, ba za a sake amfani da duk wasu kaya da aka samar a kamfanonin da ke goyon bayan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ba."

Kurtulmus ya ƙara da cewa "Daga yanzu ba za mu sake sayen wani abu daga gare su ba, kuma za mu jefar da wanda muka riga muka saya."

Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa kan Zirin Gaza bayan da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai mata wani hari a kan iyaka.

Sakamakon rikicin, aƙalla Falasdinawa 10,328 da suka hada da yara ƙanana 4,237 da mata 2,719 aka kashe. 'Yan Isra'ila da aka kashe kuma sun kai 1,600.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us