Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya, Emine Erdogan, ta rubuta wasiƙa zuwa ga Uwargidan Shugaban Ƙasar Amurka, Melania Trump, tana roƙonta da ta nuna irin damuwar da ta nuna wa yaran Ukraine waɗanda yaƙi ya shafa ga yaran Gaza.
A cikin wasiƙar da aka rubuta a ranar 22 ga Agustan 2025, Uwargidan Erdogan ta ambaci goyon bayan da Melania Trump ta nuna a baya, tana jaddada tausayi da ta nuna ga yara 648 'yan Ukraine da suka rasa rayukansu a rikicin.
Ta roƙi Melania da ta mayar da hankali kan wahalhalun da ake ci gaba da fuskanta a Gaza, inda aka yi kiyasin cewa mutane 62,000, ciki har da yara 18,000, sun rasa rayukansu cikin shekaru biyu da suka gabata.
‘Dole ne a kare yara’
Ta tuna ganawarsu a Fadar White House shekaru shida da suka gabata, inda Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya ta yaba da tausayi da damuwa game da bil’adama da Melania Trump ta nuna, wanda ya bayyana a cikin wasiƙarta ta baya-bayan nan zuwa ga Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin. Ta ce matsayinta na jinƙai “yana ba da fata a zukatan mutane.”
Ta kuma jaddada cewa 'yancin kowane yaro na girma cikin aminci haƙƙi ne na duniya baki ɗaya, dole ne a kare shi ba tare da la’akari da wurin zama, jinsi ko addini ba
“Kalaman ‘ƙananan yaran da ba a san su ba’ da aka rubuta a kan likkafanin dubban yara na Gaza da ba a iya gano sunayensu suna haifar da raunuka masu tsanani a kan lamirinmu na bai ɗaya,” in ji ta a cikin wasiƙarta.
‘Aika wasiƙa zuwa Netanyahu’
A cikin wasiƙar, Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya ta kuma ba da shawarar cewa Melania ta aika wasiƙa zuwa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, don kawo ƙarshen rikicin.
“A waɗannan kwanakin, lokacin da duniya ke ƙara farkawa baki ɗaya da kuma amincewa da Falasɗinu ta zama muradin duniya, na yi imani da cewa kira daga gare ki a madadin Gaza zai cika wani nauyi na tarihi ga al’ummar Falasɗinu,” in ji ta.
Emine Erdogan ta kammala wasiƙarta da jaddada muhimmancin kare dokokin duniya da ƙimar ɗan adam na bai ɗaya don dawo da fata ga yaran Gaza da suka tsira.
Isra’ila ta kashe kusan Falasɗinawa 62,300 a Gaza tun watan Oktoba 2023.
Harin sojan ya lalata yankin, wanda ke fuskantar yunwa. A watan Nuwamban da ya gabata, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin ɗan adam a Gaza.
Isra’ila tana kuma fuskantar shari’ar kisan kare dangi a Kotun Ƙoli ta Duniya saboda yaƙin da ta yi a yankin.