TURKIYYA
1 minti karatu
Turkiya ta yi nasarar gwajin Simsek, wani jirgi maras matuƙi mai matuƙar gudu
Jirgin wanda ake harbawa kamar roka, ya tashi daga ƙasa a karon farko, kuma za a iya amfani da shi a matsayin jirgi domin kai hari da kuma wurin kai harin ƙunar baƙin-wake.
Turkiya ta yi nasarar gwajin Simsek, wani jirgi maras matuƙi mai matuƙar gudu
Wannan matakin ya zama shaida mai ƙarfi game da irin fasahohin da aka samar a cikin gida / Other
23 Agusta 2025

Turkiyya ta samu nasarar gwajin wani sabon nau’in jirgi maras matuƙi mai suna Simsek, wanda ke da tsananin sauri, kamar yadda wani babban jami'in tsaro ya bayyana.

Jirgin wanda ake harbawa kamar roka, ya tashi daga ƙasa a karon farko, kuma za a iya amfani da shi a matsayin jirgi domin kai hari da kuma wurin kai harin ƙunar baƙin-wake, in ji Haluk Gorgun, shugaban Ma'aikatar Masana'antar Tsaro ta Turkiyya, a dandalin sada zumunta na Turkiyya, NSosyal.

"Masana'antar tsaronmu ta ƙara wani muhimmin fasaha a cikin kayan aikinta," ya rubuta.

Wannan matakin ya zama shaida mai ƙarfi game da irin fasahohin da aka samar a cikin gida, wanda ke ƙara nuna yadda Turkiyya ke da ƙarfi da kuma ikon tsoratar da abokan gaba, in ji shi.

"Muna ci gaba da tafiya tare da jajircewarmu wajen samar da mafita ta hanyar ƙera abubuwan tsaro da ake buƙata a nan gaba,” in ji shi.

Ya kuma gode wa Kamfanin Kera Jiragen Sama na Turkiyya (TUSAŞ), wanda ya samar da Simsek.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us