Mai ɗakin shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta ja hankalin duniya sakamakon wasikar da ta rubuta wa Melania Trump, inda ta yi kira ga mai ɗakin shugaban Amurka ta nuna jinƙai ga yaran Gaza kamar yadda ta yi ga yaran da rikicin Ukraine ya shafa.
Wasiƙar, wadda a cikinta ta yi kira da a ɗauki mataki kan yanayin rashin jinƙai da ake fama da shi a Gaza, ta samu karɓuwa a wajen kafofin watsa labaran ƙasashen duniya, waɗanda suka yayata kiran da ta yi na nuna tausayi da yin adalci.
Ta rubuta wasiƙar ce sakamakon matakin da tun da farko Melania Trump ta ɗauka inda ta buƙaci shugaban Rasha Vladimir Putin, ya nuna jinƙai ga yaran da rikicin Ukraine da Rasha ya shafa.
Emine Erdogan ta jaddada mawuyacin halin da ake ciki a Gaza, inda ta bayar da misali da rahotannin da ke nuna cewa na kashe yara 18,000 tare da fararen-hula 62,000 a ƙasa da sekaru biyu, tana mai yin kira ga Melania ta nuna jinƙai ga yaran Falasɗinawa tare da yin magana da firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu domin a kawo ƙarshen yaƙi.
Wasiƙar na ɗauke da saƙo na tausayi rin na uwa, kuma ya karɓu a wajen kafofin watsa labaran duniya waɗanda suka riƙa nanata kiran da Emine Erdogan ta yi na kasancewa tsintsinya maɗaurinki ɗaya a wajen yin adalci tare da fatan muryar Melania za ta zama “wani tarihi da ɗaukar nauyi” game da lamuran Gaza.
Ga yadda kafofin watsa labaran duniya suka ɗauki labarin wasikar Erdogan:
Birtaniya
BBC ta wallafa wasikar Emine Erdogan a shafinta na X, wanda ke da mabiya aƙalla miliyan 50, da kuma shafinta na Instagram wanda ke da mabiya miliya 29.4.
A ƙarkashin take mai suna, "Mai Ɗakin Shugaban Turkiyya ta yi kira ga Melania Trump ta ji tausayin yaran Gaza", BBC ta kuma wallaa labarin a shafinta na intanet.
Jaridar Telegraph ta bayar da rahoton kiran da Erdogan ta yi domin a ceci yaran Gaza, inda ta bayyana wasikar da ke jan hankalin Trump domin samar da zaman lafiya a Gaza.
Reuters ta yi amfani da taken "Mai Ɗakin shugaban Turkiyya ta buƙaci Melania Trump ta yi magana game da Gaza".
Emine Erdogan ta rubuta cewa ta aike da wasikar ce bisa matakin Melania Trump na aika tata wasikar ga shugaban Rasha Vladimir Putin tun da farko a wannan watan game da yaran Ukraine da Rasha.
A cewar kafar watsa labaran Sky News ta Birtaniya, Erdogan ta rubuta wasika ga Melania inda ta nemi ta nuna jinƙai ga aran Gaza kamar yadda ta yi ga yaran Ukraine da suka fuskanci yaƙi.
Wasikar ta nuna tausayin Melania ga yara 648 na Ukraine waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon yaƙi sannan ta yi kira ta ɗauki irin wannan mataki kan yaran Falasɗinawa.
Faransa
Jaridar Faransa ta Le Point, a cikin rahotonta mai taken “Dole ne mu haɗa muryoyinmu: Emine Erdogan ta buƙaci Melania Trump ta tallafa wa yaran Gaza,” ta bayyana cewa Erdogan ta nemi Melania da ta gana da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu game da halin da yaran Gaza ke ciki.
Jaridar Faransa ta Le Figaro, a cikin rahoton labaranta mai taken “A matsayina na uwa, mace da kuma ɗan’adam: Emine Erdogan ta kira Melania Trump da ta kare haƙƙin yaran Gaza,” ta haɗa da wannan ɓangare daga cikin wasiƙar: “A matsayina na uwa, mace da kuma ɗan’adam, ina fahimtar irin yanayin da ke cikin wasiƙarki kuma ina fatan za ki fadada irin wannan fata ga yaran Gaza waɗanda suke ƙishirwar zaman lafiya da natsuwa.”
Jamus
Kafar yada labarai ta intanet ta Jamus NTV ta rubuta rahoto da taken “Matar Erdogan ta rubuta wasiƙa mai motsa rai ga Trump.” Rahoton ya bayyana cewa Erdogan ta yi kira ga Uwargidan Shugaban Amurka da ta nuna damuwa kan yaran Gaza.
Jaridar Jamus Der Spiegel ta ce Emine Erdogan ta yi rubutu dangane da yadda ake makalawa jariran Gaza, shaidar “jariri da ba a san ko wanene ba” ya “buɗe raunukan da ba za su taɓa warkewa ba a cikin tunanimu.”
Bulgaria
Gidan talabijin mai zaman kansa mafi girma a Bulgeriya, bTV, ya wallafa wani labari wanda ya ce “Uwargidan shugaban Türkiye ta nemi Melania Trump da ta roƙi Firaministan Isra’ila ya kawo ƙarshen matsalar jinkai a Gaza.”
Girka
Kazalika kafofin watsa labaran Girka sun ɗauki labarin wasiƙar Emine Erdogan.
Jaridar EFSYN ta ruwaito cewa, "Yayin da kisan kiyashi da munanan hare-are ne faruwa a Gaza, Erdogan ta aika wasika ga Melania Trump game da halin da yaran Gaza ke ciki."
Switzerland
Jaridar 20 Minuten ta rubuta kan labarinta da cewa “Mrs. Erdogan Ta Yi Jawabi ga Mrs. Trump a Madadin Yaran Gaza.”
Jaridar ta ce, "Mai Ɗakin Shugaban Turkiyya ta yi kira ga takwararta ta Amurka ta aike da wasiƙar 'zaman lafiya' ga Benjamin Netanyahu, kamar yadda ta yi ga Vladimir Putin."
Belgium
Kafar watsa labaran da ake wallafawa da harshen Flemish a ƙasar Belgium mai suna VRT ta wallafa labarin mai taken: “Emine Erdogan ta rubuta wasika ga Melania Trump game da Gaza: ‘Ta zama maƙabartar yara’.”
"Bayan ta yi magana game da yaran Ukraine, Mai Ɗakin Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira ga takwararta ta Amurka, Melania Trump, ta yi magana game da wahalar da yara suke sha a Zirin Gaza. Ta bayyana haka ne a wata wasiƙa da ta rubuta. Shin hakan ya ja hankali? Emine Erdogan tana yawan ɗaga muryarta (game da halin da ake ciki a Gaza),” in ji labarin.
Jamhuriyar Czech
Jaridar Blesk da ake bugawa a Czech ita ma ta yi labari da kanun “Matar Erdogan ta rubuta wa Melenia Trump wasika dangane da yaran Gaza.” An rawaito cewa Erdogan ta yi kira ga Melania ta nuna tausayi ga yaran Gaza kamar yadda ta yi kan yaran Ukraine.
Bosnia da Herzegovina, Serbia da Montenegro
Klix, ɗaya daga cikin kafofin labarai da aka fi karantawa a Bosnia da Herzegovina, ta yi amfani da kanun "Sadarwa tsakanin Matan Shugaban Ƙasa".
Shafin yaɗa labarai na jaridar da aka fi karantawa a kasar, Dnevni Avaz, ya rawaito cewa, Erdogan ta aike da wasiƙa ga Melania inda ta yi bayani game da matsalar jinƙai a Gaza. Kamfanin dillancin labarai na Serbia Tanjug ya ba da cikakken bayani kan wasiƙar Erdogan na Gaza.
Blic, ɗaya daga cikin gidajen labarai da aka fi karantawa a Sabiya, ya haɗa da cikakken bayanin wasikar a cikin rahotonta na labarai mai taken "Emine Erdogan ta nemi Melania Trump ta yi tunani game da yaran Gaza."
CDM, ɗaya daga cikin gidajen labarai da aka fi karantawa a Montenegro, ya kuma jaddada cewa Erdogan ya nemi Trump ta yi tunani game da yaran Gaza.
Australia, Malaysia, Singapore da Bangladesh
Gidan labarai na Australiya 9News ya ba da rahoto kan wasiƙar da taken, “Emine Erdogan ta nemi Melania Trump da ta yi magana game da yaran Gaza.” Labarin ya faɗi abubuwan da ke cikin wasiƙar sosai.
Kafar labarai ta Free Malaysia Today da ke Malaysia ya ruwaito abubuwan da ke cikin wasiƙar.
Jaridar The Straits Times da ke Singapore ta rubuta cewa: “Emine Erdogan ta ba da saƙon cewa kiran da Melania Trump za ta yi zai zama abin tarihi ta hanyar jaddada amincewa da ƙasashen duniya suka yi wa Falasdinu.”
Hukumar labarai ta ƙasar Bangladesh, Bangladesh Sangbad Sangstha (BSS), ita ma ta yi amfani da cikakkun bayanai na wasiƙar a cikin rahotonta mai taken “Matar Erdogan ta buƙaci Melania Trump ta yi magana saboda yaran Gaza.”
Pakistan, India and Japan
Jaridar da aka fi karantarwa a Pakistan a harshen Ingilishi, Dawn, ta wallafa kiran da Erdogan ta yi wa Trump kan ta yi magana dangane da Gaza, a matsayin babban kanunta.Rubutun, ya ambato Erdogan tana cewa, “A cikin wadannan kwanaki yayin da duniya ke fuskantar kira iri daya kan a farka da kuma amincewa da Falasdinu ya zama wani fata na duniya, na amince cewa kira daga gare ki a madadin Gaza zai kuma zama sauke wani nauyi na tarihi ga Falasdinawa.”Jaridar The Times of Indiya ta yi amfani da kan labari da ke cewa “Ki yi magana saboda yaran Gaza su ma: Uwargidan Shugaban Turkiyya ta rubuta wa Melania Trump wasika, wacce ta aike wa Putin wasiƙa.”
Gabas ta Tsakiya
Wasiƙar Emine Erdogan ta kuma samu yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai a ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Al Jazeera da ke Qatar, Al Jazeera Mubasher, da tashoshi na Larabci na Al Jazeera sun ba da cikakken bayani game da wasiƙar.
Babbar jaridar Qatar Al-Arabi Al-Jadid ce ta buga labarin tare da taken "Kiran Emine Erdogan ga Melania Trump a Gaza." Rahoton ya bayyana cewa Erdogan ta ja hankali kan yaran da ke fafutukar rayuwa a ƙarƙashin hare-haren da Isra'ila take kai musu.
Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
Jaridar Sharq Al-Awsat ta ƙasar Saudiyya ce ta buga labarin tare da taken, "Matar shugaban ƙasar Turkiyya ta yi kira ga matar Trump game da yara a Gaza." Labarin ya jaddada yadda Erdogan ke fito da matsalar rashin jinƙai a Gaza.
Sky News Arabia da ke da zama a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ta watsa wasiƙar a ƙarƙashin taken "Kiran Emine Erdogan na jawo hankali ga yara a Gaza." Tashar ta bayyana kalaman Melania a cikin wasiƙar, wadda ta ba da shawarar cewa ya kamata a yi amfani da irin wannan azancin da ta nuna game da Ukraine ga yara a Gaza.
Isra'ila
Jaridar Maariv ta Isra'ila ta kawo wasiƙar Erdogan ga Melania ga masu karatunta da labarin mai taken "Daga uwargidan Erdogan zuwa uwargidan shugaban ƙasa a Fadar White House: Ku matsa wa Netanyahu." Rahoton ya bayyana cewa Erdogan ta bukaci Trump da ta tallafa wa yaran Gaza.
Jaridar Yedioth Ahronot ta ɗauki labarin mai taken "Matar Erdogan ga Melania: Aika wasika ga Netanyahu shi ma".
Falasdinu
Jaridun Falasdinawa Alkuds Alarabi, Quds al-Ihbariyya, Kamfanin dillancin labarai na Shehab da Alhadath sun yi cikakken bayani game da wasiƙar Erdogan. A cikin labaransu, sun ambato Erdogan ta jaddada cewa "An tauye hakkokin yaran Gaza."