WASANNI
2 MINTI KARATU
CAF za ta yi bincike kan rikicin da ya faru bayan wasan Maroko da DRC a Gasar AFCON
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala wasan inda keftin ɗin DRC Chancel Mbemba da kocin Maroko Walid Regragui suka fara fada.
CAF za ta yi bincike kan rikicin da ya faru bayan wasan Maroko da DRC a Gasar AFCON
CAF ta ce ba za ta yi wani karin bayani ba har sai ta kammala bincike. / Hoto: CAF / Others
23 Janairu 2024

Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan wani faɗa da aka yi bayan wasan da aka yi tsakanin DRC da Maroko inda ƴan wasa da jami’an kwallon ƙafa suka shiga rikicin.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala wasan inda keftin ɗin DRC Chancel Mbemba da kocin Maroko Walid Regragui suka fara fada. Rikicin ya haifar da cece-kuce tsakanin 'yan wasa da jami'an kungiyoyin biyu da suka ci gaba da barin filin.

Bayan nan, CAF ta fitar da sanarwa kan lamarin inda take cewa:

“CAF ta kaddamar da bincike kan Royal Moroccan Football Federation da kuma Congolese Association Football Federation bayan wani lamari da ya faru bayan wasa a Gasar AFCON ta CAF da TotalEnergies a Cote d’Ivoire tsakanin Maroko da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo. “CAF ba za ta yi wani karin bayani kan wannan lamarin ba har sai an kammala bincike.”

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us