AFIRKA
3 MINTI KARATU
Yadda mayaƙan Boko Haram suka kashe gomman mutane a garin Mafa na jihar Yobe
Harin dai na ramuwar gayya ne kan zargin kisan da ‘yan banga a Mafa suka yi wa wasu mayaƙan Boko Haram biyu, kamar yadda rundunar ‘yan sandan yankin ta bayyana.
Yadda mayaƙan Boko Haram suka kashe gomman mutane a garin Mafa na jihar Yobe
Bayan harbin kan mai uwa-da-wabi a kasuwa da kuma kona gine-gine a grain, mayakan sun fatattaki wasu mazauna cikin daji inda suka harbe su, in ji wani jami'in 'yan sanda. / Hoto: Reuters  / Others
4 Satumba 2024

Ƙungiyar Amnesty International ta ce mutum 127 ne suka mutu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne suka kai a garin Mafa da ke jihar Yobe a Arewa Maso Gabashin Nijeriya.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Abuja, babban birnin ƙasar.

Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya ce kawo yanzu ba su tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba, ko da yake wani jami'i a garin Bulama Jalaluddeen ya ce adadin ya kai mutum 81

Dungus ya ce mayaƙan Boko Haram sun yi ramuwa ne kan kisan da suke zargi 'yan banga sun yi wa wasu mayaƙansu biyu.

"Mayaƙan Boko Haram kimamin 150 ɗauke da manyan bindigogi da na'urorin harba bindigogi a kan babura fiye da 50 sun kai hari a Mafa ranar Lahadi. Sun kashe mutane da dama tare da ƙona shaguna da gidaje, sai dai har yanzu ba mu tantance yawan mutanen da suka mutu ba," in ji Abdulkarim Dungus.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi Allah wadarai da harin, sannan ya buƙaci jami'an tsaro su ƙara ƙaimi wajen murƙushe masu tayar da ƙayar baya.

Jihar Yobe dai na ɗaya daga cikin jihohi uku da suka kwashe tsawon shekaru 15 suna fama da hare-haren mayaƙan Boka Haram.

Dubban 'yan Nijeriya ne aka kashe tare da raba sama da miliyan biyu da matsugunansu.

Asarar rayuka masu yawa

Wani jami'in sojin Nijeriya da ya raka kwamandan rundunar sojoji a jihar ta Yobe zuwa Mafa, ya ce an dasa bama-bamai a hanyar shiga garin, sai dai sojoji sun yi nasara kwance su.

“Mun samu gawawwaki 37 waɗanda muka kai su babban asibitin Babangida,” in ji jami’in wanda ya buƙaci a sakaye sunanshi saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai.

Wani mazaunin garin Modu Mohammed, ya ce mazauna garin da dama sun ɓace, kana ya ƙiyasta adadin mutane fiye da 100 da suka mutu.

Ya ƙara da cewa, har yanzu akwai gawawwaki a cikin daji.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us