AFIRKA
2 MINTI KARATU
Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta musanta kai wa masallaci farmaki a Kaduna
Rundunar sojin saman ta Nijeriya ta bayyana cewa kai farmaki a yankin ya biyo bayan samun bayanan sirri daga majiyoyi masu ƙwari da dama.
Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta musanta kai wa masallaci farmaki a Kaduna
Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Hoto / Nigeria Air Force / Others
1 Oktoba 2024

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya a ranar Litinin ta dage cewa mutane 24 da aka kashe yayin farmaki ta sama a wani ƙauye da ke Kaduna 'yan ta'adda ne.

Mazauna ƙauyen Jika da Kolo da ke ƙaramar hukumar Giwa sun ce mutanen da aka kashe a farmakin na ranar 27 ga Satumba masallata ne a wani masallacin kasuwa.

Mataimakin Daraktan Hulda da Kafafen Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Saman Nijeriya, Kabiru Ali ya ce yankin ya zama matattarar 'yan ta'adda tsawon shekaru.

"An jawo hankalin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ga wasu rahotanni da ke zargin kashe mutane bayan nasarar farmaki ta sama da aka kai wa 'yan ta'adda a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna," in ji shi.

Ƙwararan bayanan sirri

Ali ya bayyana cewa sun kai farmaki a yankin ne bayan samun bayanan sirri daga majiyoyi masu ƙwari da dama, tare da tabbatar da yin kai komon leƙen asiri a wajen.

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ba ta ɗauki wannan zargi da wasa ba, a yayin da take mayar da hankali don samun nasarar farmakai ba tare da yin wata ɓarna ba, ana aiki don tabbatar da gaskiyar lamarin, kuma za a sanar da jama'a sakamakon binciken bayan kammalawa.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us