AFIRKA
2 MINTI KARATU
'Yan bindiga sun kashe fararen hula 24 a Jamhuriyar Nijar
Wasu mutane dauke da makamai sun kashe fararen hula 21 a Jamhuriyar Nijar – An kai harin ne a ranar 5 ga watan Disamba a mahadar kan iyaka tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso, in ji kafar yada labarai ta gwamnati.
'Yan bindiga sun kashe fararen hula 24 a Jamhuriyar Nijar
An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan ayarin motocin jigilar kayayyaki a kusa da Tera.   / Hoto: AA
9 Disamba 2024

An kashe fararen hula 21 a makon da ya gabata yayin wani hari da aka kai kan ayarin motocin jigilar kayayyaki a kusa da Tera, a yammacin Nijar, yankin da ake yawan fuskantar hare-haren mutane masu dauke da makamai, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a karshen mako.

Gidan rediyon gwamnati Voix du Sahel ya tabbatar da cewa an kai harin ne a mahadar iyakar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

"Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wa motocin da ke dawowa daga kasuwar mako-mako a Tera hari a ranar 5 ga watan Disamba, a yankin mai tazarar kilomita 12 a arewa da Tera, kusa da Bankilare," in ji shi.

Sojojin Nijar na kai hare-hare da dama kan kungiyoyin jihadi a yankin Tillaberi, inda ake alakanta wadannan hare-hare da "yan ta'adda."

MAJIYA:AA
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us