Ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce tana shirin kafa runduna mai dakaru 260,000 domin yaƙar ta’addanci.
Shugaba hukumar ƙungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hanan a taron manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka na shekarar 2025 a Abuja.
Jigon taron shi ne “Yaƙi da barazana ga zaman lafiya da tsaron Afirka na wannan zamanin: muhimmancin dabarun haɗin kai na tsaro.”
Touray, wanda ya samu wakilcin kwamishina mai kula da harkar siyasa da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce wannan wani ɓangare ne na rage tushen ta’addanci da sauran na’o’i na rashin tsaro a yankin.
Ya ce baya ga matakin na yaƙar ta’adanci, ƙungiyar tana ƙoƙarin aiwatar da tsarinta na tsaron ruwa, yana mai cewa babu wani yanki na Afirka da ya tsira daga matsalar ta’addanci da yaƙe-yaƙe da kuma rashin ci-gaba.
Ya bayyana cewa ƙungiyar tana buƙatar dala biliyan 2.5 domin kafa rundunar yaƙi da ta’addancin domin ba da tallafi na gudanarwa da kuɗi ga dakaru da ke bakin daga a ƙasashen da ke fuskantar ta’addanci.
Ya ce tashe-tashen hankulan ka iya kasancewa na cikin gida, amma suna buƙatar mataki na haɗaka na nahiya, inda ƙungiyar Tarayyara Afirka (AU) za ta yi aiki a matsayin cibiyar gudanarwa na waɗannan matakan.
“Babu shakka game da cewa Afirka Ta Yamma, musamman yankin Sahel, ya kasance inda ta’addanci duniya ya fi ƙamari, inda bincike ya nuna cewa yankin sahel ya samu ƙshi 51 cikin 100 na mace-macen ta’addanci a shekarar 2024 kawai,” in ji shi.