Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Nijeriya, NAHCON ta ce ta cim ma matsaya ita da ƙasar Saudiyya kan sharuɗɗa da dokoki da aka sanya wa ƙasar game da Aikin Hajjin 2026.
A wata sanarwa da NAHCON ta fitar a ranar Talata, ta ce an kai wannan gaɓa bayan wani taro ta intanet da ta yi da hukumomin Saudiyya, wanda muƙaddashin Darakta Janar na Hukumar Hajji da Umara ta Saudiyya, Ustaz Abdallah Ash Shihry ya jagoranta a ranar Litinin, 25 ga watan Agustan 2025.
Sharaɗi na farko da Saudiyya ta sanya shi ne cewa 4 ga watan Nuwamban 2025 ce za ta zama rana ta ƙarshe da ta sanya don kammala tanadar tantuna a filin Arafa da biyan kuɗinsu da kuma kammala duk wasu shirye-shiryen ba da kwangilar ayyuka.
Sai kuma ranar 1 ga watan Fabrairu da aka sanya a matsayin rana ta ƙarshe ta ɗora dukkan bayan kwangilolin harkokin sufuri da na masauƙai a kan manhajar Nusuk Masar.
Ranar ɗaya ga watan Ƙaramar Sallah, wato Shawwal ne kuma ta ƙarshe wajen ba da bizar Aikin Hajji, inda wakilan Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudiyyan suka jaddada cewa ba za a sauya ranar ba.
Jami’an ma’aikatar sun koka kan yadda aka sha samun matsaloli daga ɓangaren Nijeriya kamar na yin latti wajen kammala shirye-shirye, suna mai cewa irin hakan ka iya jawo mummunan tasiri a kan walwala da jin daɗin alhazan ƙasar.
Sharaɗi na huɗu shi ne wanda hukumomin Saudiyyar suka roƙi NAHCON cewa su tunawa maniyyata illar take dokokin biza.
Sun ce duk wanda aka kama yana Aikin Hajji ba tare da bizar Hajjin ba, to zai biya tarar riyal 20,000, kwatankwacin Naira N8,158,344, sannan zai sha ɗauri a gidan yari.
Batun yankan layya shi ne sharaɗi na biyar, inda Ma’aikatar Hajji da Umarar ta ce dole ne a biya dukkan kuɗaɗen yankan dabba na layya da kuma na biyan masauƙai ta manhajar Nusuk Masar.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Nijeriyar dai ta tabbatar wa hukumomin Saudiyya cewa za ta tsaya kai da fata don ganin cewa ta ba da haɗin kai a dukkan wasu shirye=hiryen da za su samar da walwala ga mahajjatan ƙasar.
Sannan NAHCOn ɗin ta sha alwashin bin dukkan dokoki da sharuɗɗan Saudiyya don ganin an yi Aikin Hajjin 2026 cikin aminci da nasara.