Gwamnatin Nijeriya ta yi nasarar kubutar da mutum 128 daga hannun ‘yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.
Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.
A cewar Ribadu, aikin ceton ya nuna sabbin dabarun tsaron kasa da kuma irin namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi.
Ya ce za a kula da lafiyar mutanen da aka ceto da kuma ba su tallafi don komawa cikin iyalansu da al'ummominsu.
Ribadu ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar sojoji, ‘yan sanda, jami’an leken asiri, da sauran hukumomin da suka yi aikin ceton.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace domin yaƙar ‘yan fashi da ta’addanci.
Mallam Ribadu ya buƙaci shugabannin addinai, shugabannin siyasa, kungiyoyin farar hula, da masu fada a ji a cikin al’umma da su tashi tsaye wajen kawar da rarrabuwar kawuna, su hada kai don magance kalubalen rashin tsaro.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da bin diddigin wadanda ke addabar ‘yan kasa tare da hukunta su.
Ribadu ya ce, "Za mu farauto su, mu nemo su, kuma za mu gurfanar da su a gaban ƙuliya - ko kuma su makomarsu ta zama kamar ta magabatansu da sojojinmu suka kawar da su."
Ana sa ran za bai wa mutanen da aka ceto din kulawa ta musamman don kawar musu da firgicin da suka samu kansu a ciki yayin da suke hannun ‘yan bindigar.
Gwamnati ta jaddada kudirinta na samar da yanayi na tsaro ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya tare da tabbatar da cewa kowace al’umma ta kasance cikin koshin lafiya, kuma kowane dan kasa zai iya rayuwa cikin ‘yanci da tsira daga barazanar ‘yan fashi da ta’addanci.