Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a garin Asham, kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Imo Onyekwere ya fara wallafa faruwar lamarin kai-tsaye ta bidiyo a shafinsa.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna.
A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda taragun jirgin suka tuntsura, kuma mutane sun taru a wajen suna kallon abin da ya faru da ƙoƙarin aikin ceto, yayin da wasu da suka fi kama da fasinjoji na tsaye cirko-cirko.
Hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya, NRC ta ce tuni an tura tawagogin agaji da na jami'an lafiya don kai waɗanda suka jikkata asibiti.
Sannan ana tsara yadda za a mayar da sauran fasinjojin Abuja.
Kazalika babu bayanai kan mutuwa ko jikkata sakamakon hatsarin.
Titin jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja na daga cikin mafiya zirga-zirga a ƙasar, kuma a shekarun baya bayan nan ya sha cin karo da matsaloli, ciki har da na harin da ‘yan bindiga suka taɓa kai masa a watan Maris ɗin 2022.