Jam’iyyar Adalci da Ci Gaba (AK Party) da aka kafa ta a ranar 14 ga Agustan 2001, karkashin jagorancin Recep Tayyip Erdogan ta cika shekaru 24 a siyasar Turkiyya, inda ta dinga nasara a dukkan zabukan gama gari da ta shiga.
A bikin cika shekaru 24 na jam’iyyar, Mataimakin Shugaban AK Party, Faruk Acar, ya sanar da cewa za a karbi sababbin mambobi yayin shagulgulan.
Yayin wani taron manema labarai, Acar ya jaddada cewa duk da shekaru 24 da jam’iyyar ta yi, tana nan da kuzari kuma tana ci gaba da bin burinta da manufofinta.
Ya bayyana AK Party ba kawai a matsayin wata jam’iyya ba, amma a matsayin wani gagarumar fafutuka ta jama’a, yana mai cewa, “Watakila ya dace mu bayyana cewa, ba kamar bikin cika shekaru 24 ba, za mu ci gaba da tafiya tare da karfin da muke samu daga jama’a da goyon bayan da muke karba daga al’umma.”
“A karon farko a shekararmu ta 25, za mu shiga wani zangon yakin neman zabe na shekara guda. Manufar wannan yakin neman zabe, wanda zai fara gobe, ita ce mu tafi tare da al’ummarmu kuma mu tunatar da su abubuwan da jam’iyyar da ta kai shekaru 25 ta cim ma a cikin shekaru 25 da suka gabata, inda ta yi tasiri a Turkiyya da miliyoyin ayyuka da shirye-shiryen da ta samar.”
Tun lokacin da aka kafa ta a ranar 14 ga Agusta, 2001, AK Party ta fara jan hankalin jama’a karkashin jagorancin Erdogan, wanda a lokacin shi ne magajin garin birnin Istanbul.
An zabe shi a matsayin Firaminista a shekarar 2003, sannan ya zama Shugaban Kasa tun daga 2014.
A ranar 3 ga Nuwamban 2002, jam’iyyar ta samu gagarumar nasara, inda ta lashe kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar dokoki — wani rinjaye da ba a taba gani ba cikin shekaru fiye da goma.
AK Party ta shiga zabuka guda bakwai — a shekarun 2002, 2007, 2011, 2015 — da zabukan gaggawa a watan Nuwamban 2015, Yunin 2018, da kuma na baya-bayan nan a watan Mayun 2023 — tana samun nasara a dukkan su.
Tun daga kafuwar jam’iyyar karkashin jagorancin Erdogan a 2001, Turkiyya ta zama wata babbar kasa mai tasiri a duniya, tana daukar hanyar siyasa mai fadi kuma mai cike da kuzari wajen harkokin kasa da na yankuna.
A tsawon shekaru, Turkiyya ta karfafa dangantakarta da kasashen Turai da Turkawa, da Musulmai, tana kuma daukar matsayin jagora a harkokin yankuna.
Haka kuma, ta fadada dangantakarta da sauran manyan kasashen duniya, tana kara matsayinta a matakin duniya.
Tare da wannan tsari, ta fara bayar da gudunmawa wajen warware matsalolin duniya da kuma taka muhimmiyar rawa a kungiyoyin kasa da kasa.