Ya bayyana a fili cewa Majalisar Dinkin Duniya tana bukatar gyare-gyare masu muhimmanci don ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora mata, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a cikin wani saƙon bidiyo a bikin cika shekaru 80 na wannan ƙungiyar ta duniya.
“Wajibi ne a kanmu gaba ɗaya mu tabbatar da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta zama dandali da ke wakiltar adalci na duniya a gaban zaluncin da ake yi wa Falasɗinawa,” in ji Erdogan a ranar Litinin.
Ya jaddada cewa dole ne a ɗauki matakai, da irin ƙudurin da waɗanda suka kafa wannan ƙungiya shekaru 80 da suka gabata suka nuna, don ƙarfafa Majalisar Dinkin Duniya ta yadda za ta iya dawo da zaman lafiya, wadata, amincewa da juna, da haɗin kai a duniya, tare da kai ta zuwa gaba.
Erdogan ya kuma tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga duk wani yunƙuri na gyara, ciki har da shirin UN 80 Initiative wanda aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin Babban Sakatare.
Ya ce Ankara ta himmatu wajen shiga cikin ƙoƙarin da ake yi na sauya Majalisar Dinkin Duniya zuwa tsari mai inganci, tasiri, da kuma ƙarfin kuɗi.
Dawo da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin 'fatan ɗan’adam'
Ya tunatar da kiran Turkiyya na gyaran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, yana cewa: “Muna maimaita takenmu, 'Duniya ta fi biyar girma,' bisa gyaran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, kuma muna cewa, 'Akwaiyiwuwar samun duniya mai adalci.”
“Ina kira ga ƙasashe mambobi su ɗauki matakai nan take da za su dawo da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin fatan ɗan’adam,” ya ƙara da cewa.
Shugaban Turkiyya ya kuma taya Majalisar Dinkin Duniya murnar cika shekaru 80, yana mai cewa wannan ƙungiya, wadda Turkiyya ta kasance ɗaya daga cikin mambobin da aka kafa ta da su, ta cim ma nasarori masu yawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya da kuma inganta haɗin kai tsakanin ƙasashe tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1945.
Ya miƙa fatan alheri ga wannan ranar tunawa da cika shekaru 80, yana mai addu’ar ta zama alheri ga dukkan ɗan’adam.