Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki rawar da Isra'ila ke takawa a rikicin baya-bayan nan a garin Sweida na kasar Syria, inda ya bayyana damuwar Turkiyya game da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin Syria.
"Daya daga cikin manyan masu taka rawa a bayan wannan bakin hoto (na al’amuran Sweida) ita ce Isra'ila," in ji Fidan yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Ministan Harkokin wajen Syria Asaad Hassan al Shaibani a Ankara ranar Larabar nan.
Ya kuma jaddada manufar Turkiyya game da Syria bayan rikici, yana mai cewa: "Ya kamata sabuwar Syria ta zama Syria da dukkanin al'ummomi, akidu, da al'adu ke samun kariya, kuma za su iya rayuwa tare.
“A matsayinmu na Turkiyya, muna bayar da shawarwarinmu ta wannan mahanga."
Fidan ya yi gargadin cewa Ankara na shaida abubuwan da ba za ta iya jure kallon su haka kawai ba.
Ya ce, “'yan ta'addar YPG ba su bar Syria ba, bai kamata su yi tunanin ba ma ganin haka.”
Ministan ya yi kira ga kungiyar YPG da ta gaggauta kawo karshen barazanar da take yi wa Turkiyya da kuma yankin, inda ya bukaci su da mayakansu da suka dakko daga kasashen waje da su fice daga yankin Syria ba tare da bata lokaci ba.
Ministan harkokin wajen Syria Asaad al Shaibani ya bayyana yadda kasashen ketare ke ci gaba da shiga tsakani a kasar ta Syria, yana mai bayyana wasu a matsayin "masu aiki kai tsaye da kuma neman raunana kasar ta Syria da haifar da wanzuwar wata kasa mai rauni".
Ya kuma ce al'ummar Druze har yanzu wani bangare ne na al'umar Syria, yana mai watsi da ikirarin Isra'ila da ke nuna akasin haka.
"Babu wata niyya ta ware su ( al'ummar Druze) ta kowace hanya," in ji shi. Ya kara da cewa "Abin da ya faru a Sweida Isra'ila ce ta ingiza shi don haifar da rashin jituwa a yankin."
Ya kara da cewa, "Muna da bukatu iri guda da fuskantar barazana iri daya da Turkiyya, kuma ya yi gargadi kan goyon bayan rikici a Syria.
Al Shaibani ya ce ya dauki "Babban Taron Hasakah", wanda sassan arewa maso gabashin Syria suka gudanar a matsayin taron da ya sabawa yarjejeniyar da aka kulla a ranar 10 ga Maris da kungiyar ta'adda ta YPG.
A ranar 10 ga watan Maris, fadar shugaban kasar Syria ta sanar da rattaba hannu kan yarjejeniyar shigar da dakarun ‘Syrian Democratic Forces’ (SDF) cikin cibiyoyin gwamnati, tare da tabbatar da hadin kan yankunan kasar tare da yin watsi da duk wani yunkurin raba kan kasar.
SDF dai na karkashin ikon kungiyar ta'adda ta YPG, reshen ta'addar PKK na Syria.
Gwamnatin Syria na kara zafafa ayyukan tsaro tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al Assad a bara bayan shafe shekaru 24 tana mulkin kasar.
Assad, shugaban Syria na kusan shekaru 25, ya gudu zuwa Rasha a watan Disamba, wanda ya kawo karshen mulkin Jam’iyyar Baath, wanda ke kan karagar mulki tun 1963.
A watan Janairu, an kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin shugaba Ahmad al Sharaa.