A lokacin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya sauka a birnin Mogadishu a shekarar 2011, Somalia ta kasance a cikin yanayi mafi koma baya. Fari da tashe-tashen hankula sun jefa al’ummar kasar ta gabashin Afirka mai mutane miliyan 18 cikin halin yunwa. Babu wani shugaba daga wajen Afirka da ya ziyarci kasar a cikin kusan shekaru 20.
Zuwan na shugaba Erdoğan ba wai wata manufa ce kawai ta siyasa da tattalin arziki ba, ta zama mafarin hadin gwiwa da zai sauya fasalin ka'idojin hulda da Afirka.
A cikin shekaru 14 tun bayan wannnan ziyara, 'yan kwangilar Turkiyya sun aiwatar da ayyuka 2,031 da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 97 a fadin nahiyar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Kamfanin jirgin saman Turkiyya na sauka da tashi a biranen Afirka 62 da ke kasashe 41. Daliban Afirka kimanin 62,000 ne ke karatu a jami'o'in Turkiyya.
Daga ingantaccen layin dogo na Tanzania, wanda aka amince da shi a matsayin hanyar layin dogo mafi ci gaban fasaha a Afirka, zuwa cibiyar taro ta Kigali da ke Rwanda, filin wasannin tsalle-tsallen Olympics a Senegal mai kujeru 50,000 da filin jiragen sama na Blaise Diagne da ke Dakar, kamfanonin Turkiyya sun taimaka wajen sauya fasalin ababen more rayuwa a Afirka.
Hadin gwiwar Turkiyya da nahiyar ba ta kare da kankare da karfe ba. Gidauniyar Maarif a yanzu tana gudanar da makarantu a kasashen Afirka 27.
Shugaba Erdoğan ya kai ziyara kasashe 31 na Afirka sau 53, lamarin da ya sa ya zama shugaba daya tilo a duniya da ya fi kowanne ziyartar nahiyar. Ankara ta yi imanin cewa tsarinta ya ta'allaka ne kan tarihi, fahimtar juna da hadin gwiwa inda bangarorin biyu ke cin moriyar juna, sabanin yadda kasashen Yammacin Duniya suka tsara kan tarihin mulkin mallaka da kwashe albarkatu.
Abubuwan da suka kawo bambance-bambance
"Afirka tana da fa'ida mai yawa. Ita ce nahiyar da ta fi kowacce arziki a fannin albarkatun kasa. Tare da aniyar Turkiyya na bayar da fasahohinta da bude kofa ga kasashen Afirka, nahiyar na da damar yin amfani da ita a matsayin abokiyar da aka fi so a tsakanin kasashe da dama," Ibrahim Mukhtar, kwararre kan huldar Turkiyya da Afirka ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
Wani jami'in diflomasiyyar Turkiyya, malamin jami’a kuma marubuci, Farfesa Ahmet Kavas, yana ganin dangantakar na da bambanci da kawancen gargajiya da aka saba gani.
"Dangantaka cude ni in cude ka ce da Afirka. Turkiyya na amfana a lokacin da take amfanar da sauran kasashe. Sau da yawa, Afirka tana samun mafi ƙarancin lokacin yin hulɗa da sauran ƙasashe. Dole ne a samu daidaito, wanda ke nufin raba daidai da kashi 50 kowanne ko aƙalla kashi 40 da kashi 60. A Afirka, galibi ma bai kai kashi 10. Kasashen Turai da wasu ƙasashen Asiya suna can don diban albarkatun ƙasa," in ji shi.
Misalin Somalia
Haɗin gwiwar da Somaliya ke yi da Turkiyya ta nuna yadda wannan dangantakar ke aiki.
"Na yi imanin cewa Somalia na da damar samun wata madafa ta daban da albarkatunta," in ji Erdoğan a yayin ziyararsa ta 2011.
Abin da ya biyo baya shi ne daya daga cikin muhimman ayyukan jin kai na Turkiyya, wanda cikin sauri ya fadad zuwa babban hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Mukhtar, wanda ya kalli yadda lamarin ke gudana da idon basira, ya yi imanin cewa, Turkiyya ta bayar da gudunmawa sosai wajen inganta kokarin gudanar da ayyuka a fadin Afirka. "Turkiyya ta taka rawar gani wajen sake gina wa da tallafa wa cibiyoyin gwamnati bayan yakin basasa na tsawon shekaru, wadannan cibiyoyi sun hada da ma'aikatu har zuwa majalisar dokoki.Turkiyya ba ta tantamar yin hakan," in ji shi.
A shekarar da ta gabata ne Turkiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Somaliya don samar da kayan aiki da sake gina wa da horar da sojojin ruwan Somaliya. Wannan wani kari ne ga sansanin TURKSOM, sansanin sojin Turkiyya da aka kashe dala miliyan 50 don kafa shi a Mogadishu a shekarar 2017 don horar da sojojin Somaliya.
Shekaru 100 na mu’amala
Alakar Turkiyya da Afirka ta koma wa ga lokacin Daular Usmaniyya, musamman a Arewaci da Gabashin Afirka. A shekarun 1960, yayin da kasashen Afirka suka dinga samun 'yancin kai, Turkiyya ta amince da sabbin kasashe kuma ta goyi bayan kawar da tsarin mulkin mallaka.
Habakar wannan dangantaka ta samo asali ne lokacin da Ankara ta ayyana 2005 a matsayin "Shekarar Afirka".
"Bayan kaddamar da shirin, Turkiyya ta yi amfani da hakan a matsayin wata dama ta raya dangantakarmu da nahiyar Afirka, kusan shekaru 20 kenan muna Afirka, muna da ofisoshin jakadanci goma sha biyu kacal a nahiyar ya zuwa shekarar 2009. A halin yanzu, Turkiyya na da ofisoshin jakadanci 44, wanda hakan ya sa ta zama a matsayi na hudu a fannin diflomasiyya a Afirka bayan China, wadda ke da ofisoshin jakadanci 52, da Amurka da ke da 50 da Faransa da ke da 47."
Tarayyar Afirka ta baiwa Turkiyya matsayin babbar kawa a Kungiyar a shekarar 2008. Tun daga wannan lokacin, kasashen Afirka sun kara yawan ofisoshin jakadancinsu da ke Turkiyya daga 10 zuwa 38 ya zuwa shekarar 2024, yayin da adadin ofisoshin jakadancin Turkiyya a kasashen Afirka ya karu daga 12 a shekarar 2002 zuwa 44 a shekarar 2024. Yawan ziyarar da bangarorin biyu suka kai a cikin shekaru 5 da suka gabata ya hausa sau 500.
Hukumomin Turkiyya irin su TIKA da DSİ da Gidauniyar Diyanet da kuma Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent na Turkiyya sun gina daruruwan rijiyoyi a fadin Najeriya da Habasha da Sudan da Mali da Burkina Faso da Somalia.
Hukumar Hadin Kan Da Gudanar da Ayyuka ta Turkiyya (TİKA) na da ofisoshi 22 a Afirka kuma ta gudanar da ayyuka a fannoni da dama, kamar kiwon lafiya da noma a nahiyar. Hukumar ta ce an aiwatar da ayyuka 1,884 daga shekarar 2017 zuwa 2022.
Ta bude ofishinta na farko a kasar Habasha a shekarar 2005, kuma tun daga lokacin ta fadada ayyukanta zuwa dukkan kasashen Afirka, tare da bayar da tallafi da dama ga ''ayyukan da suka shafi cigaban Afirka'' wadanda suka hada da kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai.
Ayyukan da TİKA ta gudanar sun hada da asibitin motsa jiki na Libya, asibitin Recep Tayyip Erdoğan na Somalia, asibitin sada zumunci tsakanin Nijar da Turkiyya da asibitin Turkiyya na koyarwa da bincike a Nyala da ke Sudan. TİKA ta kuma tallafa wa fannin kiwon lafiya a Afirka a lokacin barkewar annobar Covid-19.
In Uganda, the Turkish Red Crescent installed 20 solar-powered wells for Kayunga households. In Djibouti, DSİ built the Ambouli Friendship Dam to control flooding and support farming.
A Uganda, kungiyar agaji ta Red Crescent ta Turkiyya ta haka rijiyoyin birtsatse 20 masu amfani da hasken rana ga gidajen Kayunga. A Djibouti, DSİ ta gina madatsar ruwa don magance ambaliyar ruwa da tallafa wa ayyukan noma.
Kasuwanci na fayyace alakar
Kasuwanci tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka ya yi habaka sosai daga dala biliyan 4.3 a shekarar 2002 zuwa dala biliyan 36.6 a karshen shekarar 2024, wanda ya nuna kari har ninki tara, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Zuba jarin Turkiyya a Afirka ya karu daga dala miliyan 67 a shekarar 2003 zuwa dala biliyan 10 a shekarar 2024, yayin da ‘yan kwangilar Turkiyya suka gudanar da ayyuka 2,031 na dala biliyan 97 a fadin nahiyar.
Mukhtar ya shaida wa TRT Afrika cewa, "A halin yanzu, manyan kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa Turkiyya su ne kayayyaki noma, yayin da Turkiyya ta fi fitar da kayayyaki da aka sarrafa zuwa Afirka.”
Kamfanonin Turkiyya na ci gaba da gudanar da manyan ayyuka a kasashen nahiyar da suka hada da Afirka ta Kudu da Libya da Sudan da Burkina Faso da Togo da kuma Gambia.
Hadin gwiwar samar da tsaro
Yayin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara a fadin Afirka, Turkiyya ta zama babbar kawar samar da tsaro.
Mukhtar ya ce, "Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gwamnatocin kasashen Afirka a cikin shekaru goman da suka gabata, inda ta ke bin tsarin da ya kamata a yaba musu. A duk lokacin da Turkiyya ta shiga cikin kwantar da tarzoma ko tura kayan soja ko sojoji zuwa wani yanki na Afirka, suna yin hakan ne da izinin gwamnatin kasar."
Kayayyakin tsaro da na sufurin sararin samaniyar Turkiyya da aka fitar Afirka sun kai na dala biliyan 5.5 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 27 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Rabon kasashen Afirka a wannan ci gaban kuma ta karu matuka.
Neman Ilimi yana buɗe kofofi
Ilimi na kara bayyana ingancin tsarin Turkiyya, inda ya zuwa karshen shekarar 2024 akalla dalibai 62,000 na Afirka ne ke karatu a kasar, akasarinsu na samun tallafin karatu na gwamnatin Turkiyya, a cewar bayanai daga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
"Turkiyya na bayar da muhimmanci sosai ga ilimi. A halin yanzu, muna da kimanin dalibai 340,000 na duniya a Turkiyya, wanda akalla kashi 18 ‘yan Afirka ne. Muna da makarantun Maarif a Afirka inda kimanin yara 20,000 na Afirka ke karatu," in ji Farfesa Kavas.
Gidauniyar Maarif na gudanar da cibiyoyi sama da 230 a kasashen Afirka 27. Cibiyar Yunus Emre na gudanar da shirye-shiryen koyar da harshe da al'adun Turkiyya a cibiyoyi 18 da ke kasashe 15.
Nasir Abu Machano, Manajan Darakta na Izmir Pharmacy Ltd da ke Tanzania da kungiyar Izmir a kasashen ketare, ya fara zuwa Turkiyya ne da tallafin karatu na IDB bayan ya kammala makarantar sakandare a Zanzibar.
Yare ya zamar masa matsala, amma ya ji dadin irin tarbar da aka yi masa inda har ya zuwa yake godiya.
Machano ya ce: "Mun samu mutanen Turkiyya a matsyain masu kaunar baki. Sun taimaka mana ta hanyoyi da yawa. Sun fahimci cewa wadannan baki ne kuma sun taimaka mana mu shiga duniyarsu tare da saba wa da ita."
Ya hadu da matarsa a Izmir kuma ya koma Tanzania a shekarar 2007, inda ya sanya wa kamfaninsa sunan garin da ya yi karatu.
"Kamfanin Izmir Pharmacy ya fadada zuwa babban yankin kasar Tanzania, inda ya samar da ayyukan yi ga matasa da dama. Lokacin da muka dawo daga Turkiyya zuwa Zanzibar,babu shagunan sayar da magani da yawa. Watakila akwai kwaya bakwai kawai, daga cikinsu suna bayar da sarin kayayyaki, ba wai kananan shagunan jama\a ba.," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Manazarta na ganin alakar Turkiyya da kasashen Afirka na kara zurfafa, madalla da tsarin da ya kunshi jama'a da hadin gwiwa da kawo sauyi cikin dogon lokaci maimakon hadin kan tattalin arziki kawai.
Dangantakar ta riga ta wuce tsarin cigaba na gargajiya. Kasashen Afirka sun sami sabbin hanyoyin samun cigaba yayin da Turkiyya ke fadada mazauninta a duniya ta hanyar hadin gwiwa da aka gina bisa manufar cude-ni-in-cude-ka.