Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijar, COLDEFF, ta yi nasarar ƙwato takardar kuɗin FCFA 63,808,497,269 da kuma ƙadarori da suka kai FCFA biliyan biyar.
Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ruwaito cewa shugaban hukumar COLDEFF, Kanar Zennou Aghali Moussa, ne ya bayyana haka a ƙarshen mako a Yamai, babban birnin ƙasar.
Kanar Moussa ya yi wannan bayanin ne a gaban mambobin majalisar kare ƙasa (CNSP), kamar yadda kamfanin ANP ya ruwaito.
Da yake magana game da takardun da aka ce sun ɓace daga harabar hukumar tasa, Kanar Zennou Aghali Moussa ya ce babu gaskiya a cikin wannan maganar, yana mai cewa abin dariya ne.
"Lallai, tsarin tsaro a harabar ofishinmu ingantacce ne sosai," in ji shi.
Shugaban na COLDEFF ya ƙara da cewa, "ba ma son mu shiga wannan muhawarar, amma za ku iya yawo cikin harabarmu kuma ku ga irin matakan tsaron da ke akwai."
Kazalika shugaban hukumar ya ce za su ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa tsare-tsaren dokar da ta kafa ta.