KASUWANCI
2 minti karatu
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko.
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
A Yammacin Afirka aka fi noma koko a duniya / Reuters
3 awanni baya

Hukumar da ke kula da harkar noman koko ta ƙasar Ghana (COCOBOD) ta ce manoman koko a ƙasar sun fi takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire samun farashi mai kyau, kuma duk labarin da ya saɓa wa hakan ba gaskiya ba ne.

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba a babban birnin ƙasar Accra ta yi ƙarin haske game da wasu rahotanni da ra’ayoyin jama’ar ƙasar da ke nuna cewa farashin koko daga bakin gona a Ghana bai kai farashin koko ba a  Côte d’Ivoire.

Sanarwar ta ce alƙaluman kasuwa na yanzu da kuma sharhi na masu zaman kansu sun nuna cewa manoman koko na ƙasar Ghana suna samun kuɗi fiye da takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire.

Sanarwar ta ce, rahoton watan Agustan shekarar 2025 na cibiyar da ke sa ido kan saye da sayar da kayayyaki ya nuna cewa farashin da ake sayar da kokon Ghana ya tsaya a kan ¢3,228.75 kan ko wane buhu mau nauyin kilogiram 64 na koko (kwatankwacin ¢51,660 ga ko wane tan ko kuma $5,040.00/ ga ko wane tan).

Kazalika ta ce farashin koko daga gona a ƙasar Côte d’Ivoire ya kasance ¢2,553.38 kan ko wane buhu mai nauyin kilogiram 64 (kwatankwacin ¢40,854 ga ko wane tan ko kuma $3,886 ga ko wane tan), kuma wannan na nufin fifikon farashi na ₵675.38 a kan ko wane buhu ($64.16) da kuma ¢10,806 a kan ko wane tan ($1,154) ga manoman Ghana.

Sanarwar ta ce a bisa ko wane kilo, manoman Ghana suna samun  ¢51.65 ($5.04) maimakon ¢40.85 ($3.89) da manoman Côte d’Ivoire ke samu.

Ta ce ga ko wane buhu mai nauyin kilogiram 64, manoman Ghana suna samun $315, maimakon $227 da manoman Côte d’Ivoire ke samu a kan ko wane tan, Kokon Ghana na da darajar  $5,040, maimakon $3,630 da kokon maƙwabciyarta ke samu.

Sanarwar ta ce maimakon iƙirarin da ake cewa farashin ɗaya ne ko kuma manoman Ghana na sun fi shan wahala, farashin koko daga gona a Ghana ya fi na ƙasar da ma sauran ƙsashe a yankin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us