Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar, in ji hukumomin ƙasar a ranar Laraba.
Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339 , in ji hukumar tsaron fararen hular ƙasar.
“Wasu mutum 30 sun mutu bayan gidajensu sun rushe yayin da mutum 17 suka nutse a ruwa.
“Kazalika ambaliyar ta raunata mutum 70 ta kuma haddasa mutuwar dabbobi 257,” in ji hukumar.
Kwamiti na ƙasa da aka ɗora wa alhakin hana ambliya ya ce ya fara raba tallafin abinci ga iyalai 3,776.

Tun da fari a ranar Laraba, Ministan Ababen More Rayuwa na Nijar, Kanar Manjo Salissou Mahaman Salissou ya ce ya zuwa ranar Talata 19 ga Agustan 2025, ambaliyar ruwa a Nijar ta shafi kimanin mutane fiye da 52,000.
Kamfanin dillancin labarai na Nijar, ANP ne ya ambato cewa ministan, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Ƙasa don Kiyayewa da Kula da Ambaliya (CNPGI) ya jagoranci taron ranar Talata, a babban ɗakin taro na ofishin Firaminista.