TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya za ta ƙaddamar da layin sadarwa na 5G nan da 2026
Ana sa ran matakin na 5G zai karfafa hanyoyin sadarwa na kasar, da bayar da damar hanzarta aika bayanai da karfafa hanyoyin sadarwa.
Turkiyya za ta ƙaddamar da layin sadarwa na 5G nan da 2026
A ranar 16 ga watan Agusta ne wata doka ta shugaban kasa da aka buga a Jaridar Gwamnati ta fara gudanar da shirin na 5G a hukumance. (Photo:AA) / AA
1 Satumba 2025

Ma'aikatar Sufuri da Samar da Ababen More Rayuwa ta Turkiyya ta sanar cewa a ranar Lahadi 16 ga Oktoban 2025, Turkiyya za ta gudanar da bikin bayar da aikin assasa layin sadarwa na 5G wanda za a kaddamar da fara amfani da shi a shekarar 2026 mai zuwa.

Ana sa ran matakin na 5G zai karfafa hanyoyin sadarwa na kasar, da bayar da damar hanzarta aika bayanai da karfafa hanyoyin sadarwa.

A ranar 16 ga watan Agusta ne wata doka ta Shugaban Ƙasa da aka buga a Jaridar Gwamnati ta fara gudanar da shirin a hukumance, inda ake sa ran za a gudanar da bikin bayar da kwangilar aikin a ranar 16 ga Oktoba, a cewar ma’aikatar.

Shirin wani bangare ne na manyan tsare-tsare don bunkasa fasahohin da suka kunno kai kamar su Kirkirarriyar Basira (AI), manyan bayanai, manhajoji, motoci masu aiki da kansu, da dabarun kera kayayyaki, a cewar wani rahoto na Hukumar Fasahar Sadarwa da Bayanai (BTK).

Masana’antu daban-daban za su amfana da aikin

Gwajin da aka gudanar a dakunan gwaje-gwajen a bara ya nuna saurin layin sadarwa na 5G na gigabits 7.5 a sakan daya, yayin da ainihin hanyoyin sadarwa ke da saurin gigabits 4.7 a sakan daya.

Da zarar an tura shi, babbar hanyar sadarwar 5G za ta iya watsa bayanai cikin sauri zuwa 1 gigabit zuwa fiye da na'urori biliyan 20 da aka haɗa, yayin da manyan hanyoyin sadarwa za su tallafawa sabbin damar aiki a masana'antu daban-daban.

Har ila yau, hanyar sadarwar za ta bayar da dama ga layukan rarraba su su yi amfani da fasahar "slicing", don rarraba layukan sadarwa zuwa sassa daban-daban duba ga buƙatun kowane bangare.

Na'urorin zamani za su iya yin sadarwa ba tare da katsewa ba ko da yayin tafiya cikin sauri fiye da kilomita 500 a kowace awa (mil 310.6 a kowace awa).

Hukumar BTK ta yi tsokacin cewa hanyar sadarwar ta layukan 5G za ta kasance mafi inganci mai amfani da makamashi, wanda za ta rage yawan amfani da batir da kashi 90 cikin dari.

A halin yanzu, ana samun 5G a filayen wasanni na manyan kungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turkiyya guda huɗu, filin jirgin sama na IGA Istanbul, da kuma wurare kusan 30, gami da Babbar Majalisar Dokoki a Ankara.

Ana sa ran cikkaken shirin zai kawo sabbin damarmaki a hanyoyin sadarwa na cloud, Kirkirarriyar Basira, da Intanet.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us