TURKIYYA
2 minti karatu
Emine Erdogan ta yi kira ga ƙarfafa haɗin kan al’adu da muhalli a wajen taron SCO
Matan shugabannin kasashen Turkiyya, Nepal, Armenia, Malaysia, Mongolia, Azerbaijan, Iran, Masar da Uzbekistan, tare da ‘yar shugaban kasar Iran, sun halarci taron raya al’adu a gefen taron SCO.
Emine Erdogan ta yi kira ga ƙarfafa haɗin kan al’adu da muhalli a wajen taron SCO
Shugaban Kasar China Xi Jinping ya karbi bakuncin taro na kwanaki biyu na shugabannin kasashe mambobin SCO da SCO+ / Turkish Presidency
16 awanni baya

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta halarci wani shirin raya al'adu wanda uwargidan shugaban kasar China Peng Liyuan ta shirya a gefen taron shugabannin kasashen kungiyar SCO karo na 25.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Turkiyya ta fitar a ranar Litinin din nan ta ce, Peng ta yi kyakkyawar tarba ga Erdogan a wajen taron, inda ta kuma hadu da matan shugabannin kasashe don daukar hoto kafin halartar taron raya al'adun wanda ke nuna al'adun kasashen da ke halartar taron.

Haka kuma matan shugabannin kasashen Nepal, Armenia, Malaysia, Mongolia, Azerbaijan, Iran, Masar da Uzbekistan, tare da ‘yar shugaban kasar Iran ma sun halarci taron.

Taron ya bayar da dama ga mahalartan wajen yin musayar ra’ayoyi kan al’du da kyawawan abubuwan da suke da shi na bai daya, in ji sanarwar.

Bayan taron, Emine Erdogan ta fitar da sako ta shafin sadarwa na yanar gizo tana mai bayyana jin dadinta bisa halartar taron da Peng ta karbi bakunci.

“A wajen wannan taro na musamman inda muka shaida al’adu da kayatattun gine-gine na garin Tianjin, mun yi tattaunawa ta kawance tare da musayar ra’ayoyi kan hadin kai a bangarorin ayyukan da muke da su na bai daya, kamar zaman lafiya, iyali, muhalli da al’adu.” in ji ta.

"Ina fatan cewa wadannan taruka masu ma'ana za su karfafa alakar da ke tsakanin kasasnemu."

Shugaban Kasar China Xi Jinping ya karbi bakuncin taro na kwanaki biyu na shugabannin kasashe mambobin SCO tare da “SCO Plus,” inda aka tattara shugabannin kasashe 20, baya ga shugabannin kungoyoyin kasa da kasa.

Wannan ne taro mafi girma da SCO suka gudanar kuma karo na biyar da China ke karbar bakunci tun bayan kafa kawancen a 2001.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us