Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gana da takwaransa na ƙasar China, Xi Jinping, domin tattauna dangantakar ƙasashen biyu yayin wani taro a birnin Tianjin mai tashar ruwa.
Ganawar ta ranar Lahadi ta gudana a gefen taron koli na 25 na Ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kai ta Shanghai, inda bangarorin biyu suka mayar da hankali kan kasuwanci, zuba jari, da kuma zaman lafiya a yankin.
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa dole ne a karfafa dangantakar tattalin arziki ta hanyar zuba jari mai ɗorewa da daidaito, yana mai cewa kasuwanci kaɗai ba zai iya tabbatar da zaman lafiya na dogon lokaci ba.
“Ya kamata a tallafa wa kasuwancin kasashen biyu ta hanyar zuba jari domin tabbatar da daidaito da ɗorewa; akwai babbar dama a fannin fasahar zamani, makamashi, lafiya, da yawon shakatawa da kuma karuwar hadin kai tsakanin kamfanonin kasar China wajen zuba jari a Turkiyya domin samun alfanu,” in ji fadar shugaban kasar Turkiyya a wata sanarwa.
Shugaba Erdogan ya kuma jaddada bukatar daidaitawa tsakanin shirin Middle Corridor na Turkiyya wanda shiri ne na cinikayya wanda zai faro daga kudu maso gabashin Asia da China zuwa Turai ta Kazakhstan da Tekun Caspia da Azerbaijan da Georgia da Turkiyya da kuma shirin Shirin Belt and Road na ƙasar China domin ƙarfafa hadin kai a yankin.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da kula da tsare-tsaren tattaunawa, tare da tabbatar da ci gaba da tattaunawa akai-akai da hadin gwiwar cibiyoyi domin karfafa kawancensu.
Yayin da yake jaddada dangantakar dabarun da ke tsakanin Ankara da Beijing, Erdogan ya sake tabbatar da goyon bayansa ga manufar “China Daya Tak” (One China).
Shugabannin biyu sun kuma duba rikice-rikicen kasa da kasa, ciki har da yakin Rasha da Ukraine da halin da ake ciki na jin kai a Gaza, da kuma yiwuwar daukar matakai na hadin gwiwa game da Syria.